Da Dumi Dumi

Oshoala na kishin ruwan lashe kofuna a Barcelona

Asisat Oshoala ta ce tana kishin ruwan lashe kofuna a kungiyar mata ta Barcelona, bayan da ta ci na farko a gasar kwallon Spain.

Mai shekara 25, ta ci kwallo a wasan da Barcelona ta lallasa Real Sociedad 10-1 a ranar Lahadi, kuma hakan ya sa ta lashe Super Cup a gasar mata a garin Salamanca.

Oshola ta shaida wa BBC cewa: “Abin murna ne in kara cin kofi, bayan Copa Catalunya da na dauka a bara. Abin da na sa a gaba shi ne kwazo da samun nasarori, kuma babu abin da zai dauke hankalina kan wannan manufar tawa.’’

’Yar kwallon Najeriyar ta ci gaba da cewa “Kawo yanzu mun buga gasar rukuni da ta Zakarun Turai da kuma Kofin Spain a bana, akwai jan aiki a gaba ke nan.’’

Barcelona wadda kawo yanzu ba a doke ta ba tana ta daya a kan teburi, inda take fatar lashe kofin a karon farko bayan shekara biyar.

ADVERTISEMENT

Haka kuma Barca ta mata za ta fafata da Atletico Madrid a wasan daf da na kusa da na karshe na gasar Zakarun Turai  a watan gobe.

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya