✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Osinbajo ya amince da nadin manyan sakatarorin gwamnati 21

  Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya amince da nadin manyan sakatarorin gwamnati na dindindin. Nadin nasu ya zo ne sakamakon jarabawar da aka shirya…

 
Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya amince da nadin manyan sakatarorin gwamnati na dindindin. Nadin nasu ya zo ne sakamakon jarabawar da aka shirya wa daukacin daraktocin gwamnati.
Daga cikin wadanda mukaddashin shugaban kasa ya amince da nadin nasu akwai ’yan Arewa guda shida sai ’yan Kudu 14.
A wata takardar sanarwa da Mai Magana da Yawun Hukumar Ma’aikata ta Kasa, Mista Haruna Imrana ya raba wa manema labarai, ta nuna cewa Shugabar Mai’aikatan Gwamnatin Tarayya, Misis Winifred Oyo-Ita ce ta bayyana haka.
Ta bayyana cewa sakatarorin da aka nada sun hada da Ehuri Georgina Ekeoma daga Jihar Abia da Akpan Edet Sunday daga Jihar Akwa Ibom da Angbogu Ifeoma Nkiruka daga Jihar Anambara da Walson-Jack Didi Esther daga Jihar Bayelsa da Gekpe Grace Isu daga Jihar Kuros Riba da Aliboh Leon Lawrence daga Jihar Delta da Uwaifo Clement daga Jihar Edo da Folayan Ayodele Olaniyi daga Jihar Ekiti da Osuji Ndubusi Marcellinus daga Jihar Imo da Mu’azu Abdulkadir daga Jihar Kaduna da Sulaiman Mustapha Lawal daga Jihar Kano da Abdullahi Abdul’azeez Mashi daga Jihar Katsina da Adebiyi Bolaji Adekunle daga Jihar Legas da Ibrahim Musa Wen daga Jihar Nasarawa da Odewale Samson Olajide daga Jihar Ogun da Odesola Olusade daga Jihar Ondo da Adekunle Adeyemi daga Jihar Oyo.
Sai Nabasu Butrus Bako daga Jihar Filato da Ekaro Comfort Chukwumuebobo daga Jihar Ribas sai Umar Mohammed Bello daga Jihar Sakkwato da kuma Aduda Gbariel Tanimu daga babban birnin taraya Abuja
Sanarwar ta kara da cewa za a bayyana mukamansu nan ba da dadewa ba.
Matakin nadin sakatarorin ma’aikatun gwamnati ya fara ne da daraktoci 300 wadanda suka zauna jarabawa. Daga bisani an rage adadin zuwa 78 bayan da aka zabge daraktoci 222.
Daraktoci 78 sun zauna jarabawar kwamfuta daga bisani aka zabi guda 59 da suka sami nasara.