✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Osinbajo ya kaddamar da tsarin habaka kiwo a Adamawa

A ranar Talatar da gabata ce Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da wani tsarin habaka kiwo mai suna Shirin Sake Fasalin Tsarin Kiwo…

A ranar Talatar da gabata ce Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da wani tsarin habaka kiwo mai suna Shirin Sake Fasalin Tsarin Kiwo (National Libestock Transformation Plan NLTP) a garin Gongoshi da ke Karamar Hukumar Mayo-Belwa a Jihar Adamawa.

Osinbajo ya bayyana cewa wannan tsarin ba ya da nasaba da ruga, domin a cewarsa wannan tsarin na kiwo Kwamitin Tattalin Arzikin Kasa (NEC) ya gana da gwamnoni wajen assasa wannan tsari na kiwo.

Farfesa Osinbajo ya ce saboda rikicin makiyaya da manoma ne ya sanya ofishinsa ya assasa wannan tsari domin neman maslaha a tsakanin makiyaya da manoma.

Ya ce wannan tsari ne da bai wajaba a kan kowane Gwamna ba, illa Gwamnan da ya ga yana da filin da zai gudanar da tsarin a jiharsa.Ya ce tsarin zai taimakaw a jihohi bakwai da suka hada da; Adamawa da Benuwe da Kaduna da Taraba da Zamfara da Filato da kuma Nasarawa.

Sannan ya ce Jihar Adamawa ita ce za a fara da ita kasancewar tana da ababen da ake bukata na kiwon dabbobin musamman shanu da a cikin nau’o’in shanu da ake da su a fadin kasar, akwai guda hudu da jihar ke da su; kamar Adamawa Gudali da ba za a iya samu a ko’ina ba face a jihar.

Ya bayyana cewa wannan tsari dai za a fara gudanarwa, zai wakana ne tsakanin shekarar 2019 zuwa 2028.

Shugaban Gudanar da Shirin NLTP a Jihar Adamawa, Farfesa Alikido Boh ya ce za a yi wannan tsari ne irin na zamani sannan ya  ce Najeriya tana da mazaunan shanu 15 da a cikinsu Adamawa ke da mafi yawa.

Ya kara da cewa Gongoshi na da fili hekta 9,500 da ya dace da tsarin, ko da yake wannan tsarin zai gudana ne a waje biyar a jihar da suka kunshi Nasarawo da ke Jada da Dauchi da ke Song da Garku a Gombi da kuma Sorau a Maiha.

Boh ya ce akwai fili hekta 60,000 a wadannan kananan hukumomin da gidajen manoma 190.

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya ce wannan tsari na kiwo zai kawo mafita game da rikicin makiyaya da manoma a kasar nan.

Ya ce ganin yadda wannan rikicin ya addabi jama’arsa ne ya sanya ya yarda da tsarin da kuma ya samu goyon bayan Mataimakin Shugaban Kasa game da kaddamar da shi.