✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Osinbajo ya sake ziyartar dattijon Kubwa

A ranar Juma’ar  da ta gabata ce Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci garin Kubwa Abuja, inda ya isa gidan wani dattijo a garin,…

A ranar Juma’ar  da ta gabata ce Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci garin Kubwa Abuja, inda ya isa gidan wani dattijo a garin, wanda aka bayyana a matsayin mafi tsufa a tsakanin ’yan asalin yankin da ke garin.

Ziyarar wadda ta zo a matsayin ta bazata, an bayyanata a matsayin ta cika alkawari da Mataimakin Shugaban Kasan ya yi a lokacin da ya kawo masa ziyarar farko a watan Junairu, a yayin yakin neman zabe kamar yadda mai magana da yawunsa mista Laolu Akande ya yi karin haske daga bisani.

Wakilinmu ya tattauna da dattijon mai suna Gazazhin Alagazhin wanda ya dora a kan shekara dari, da kuma dansa mai suna Sunday a gidansu da ke Unguwar Kukwaba a garin na Kubwa. A bayanin da ya yi dattijon wanda ya kasance cikin wadanda gwamnatin tsohon shugaban kasa Babangida ta sake yi wa sauyin wurin zama bayan daukosu daga yankinsu na kaka-da kakanni da ke kusa da filin wasa na kasa na Abuja zuwa Kubwa, ya ce gidajen da a ka rabawa magidanta tare da wasu daga cikin ’ya’yansu a lokacin, a yanzu baya iya daukansu kasancewa sun hayayyafa tare da jikoki, sannan kuma gonakin da su ka mallaka duk sun koma rukunin gidaje ba su da wurin noma.

Ya ce a lokacin ziyarar ta mataimakin shugaban kasa, ya koka masa a kan lamarin tare da neman gwamnati ta yi wani abu a kai kasancewar ba su da wani waje da su ka sani in banda Abuja. Shi ma daya daga cikin ’ya’yan mutumin wanda shi ne na biyar a cikin ’ya’yansa shida da ke raye, Mista Sunday Gazazhin ya ce ya samu nasarar kammala karatun difiloma a makarantar poly ta Nassarawa sannan a yanzu haka ya na karatu a jami’ar bayan fage (Open Unibersity), sai dai a cewarsa bai sami aiki ba.

Ya ce hudu daga cikin ’ya’yan mahaifinsu na zaman takura ne a gidan mahaifin tare da ’ya’yansu, inda ya zargi hukumar kula da birnin tarayya da gaza samar masu da mahalli da kuma aikin yi duk da alkawuran da ya ce ta sha yi musu a kan batun. Mista Sunday wanda ke matsayin shugaban matasa na yankin, ya bayyana ziyarar ta Osinbajo a matsayin abin farin ciki da ba za su taba mantawa da ita ba, sannan ya ce su na sarai gwamnatin za ta cika alkawarin sama masu aikin yi da kuma karin muhalli kamar yadda ya ce mataimakin  shugaban kasa ya sha alwashin duba a kan lamari.