✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Otedola ya tallafa wa Chukwu da Naira miliyan 18

A shekaranjiya Laraba ce shahararren dan kasuwar nan Femi Otedola ya tallafa wa tsohon kocin Super Eagles, Christian Chukwu da Dala dubu 50 (kimanin Naira miliyan…

A shekaranjiya Laraba ce shahararren dan kasuwar nan Femi Otedola ya tallafa wa tsohon kocin Super Eagles, Christian Chukwu da Dala dubu 50 (kimanin Naira miliyan 18 don a yi masa magani a kasar waje.

Christian Chukwu wanda  yake kwance a wani asibiti da ke Enugu, yana fama da  rashin lafiya ne da ba a gano shi ba.

Tsohon kocin, wanda yake cikin mawuyacin hali, kimanin mako biyu ke nan da iyalansa suka koka game da yadda gwamnati da Hukumar NFF suka yi biris da shi, duk da irin gudunmawar da ya bayar game da ci gaban harkokin wasanni a kasar nan.

Jim kadan bayan iyalan sun koka ne sai Gwamnan Enugu ya ba shi tallafin Naira miliyan 2 a matsayin kudin kwanciya da na magani da na abincin iyalansa kafin a ga yadda jikin nasa zai kasance.

Sai dai duk da wancan tallafi rahotanni sun nuna kocin bai samu sauki ba, wanda hakan ya sa sai an kai shi wani asibiti a Landan don a duba lafiyarsa.

Tun farko Femi Otedola, ya yi wa kocin alkwarin Dala dubu 50 amma ganin yadda abin ya dauki lokaci ne ya sa iyalansa suka fid da tsammani, amma kwatsam a shekaranjiya Laraba sai attajirin ya cika alkwarin da ya yi wa Chukwu inda ya mika masa cekin Dala dubu 50.

Philip Akinola Shugaban Kamfanin Mai da Iskar Gas na Zenon Petroleum and Gas Limited, mallakar Femi Otedola ne ya mika cekin kudin ga iyalan Chukwu a Enugu a madadinsa.

Kafar watsa labarai ta The Cable ta kalato cewa ana sa ran a makon farko na wata mai zuwa (Mayu) ne za a kai Chukwu wani asibiti a Ingila don a ci gaba da duba lafiyarsa. Mista Philip ya tabbatar da cewa wannan tallafi da aka  ba Chukwu zai isa a duba lafiyarsa har ya dawo gida ba tare da wata matsala ba.

A wata tattaunawa da kafar watsa labarai ta The Cable ta yi da attajiri Otedola ta waya ya tabbatar da bayar da wannan tallafi ga tsohon kyaftin din Super Eagles Christian Chukwu, inda ya yi masa addu’ar samun sauki a cikin gaggawa.

Christian Chukwu ya taba yi wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles kwallo, har ya zama Kyaftin.  Sannan ya horar da kungiyoyin kwallon kafa na Super Eagles da kuma na Harambee Stars da ke Kenya.

Kafin ya kamu da rashin lafiya, yana daga cikin jami’an da ke kula da kungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangers, mallakar gwamnatin jihar.