✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Pa Adama Aduku: Rayuwa da mutuwar sojan Najeriya da ya halarci Yakin Duniya na Biyu

Dalilin sa masa sunan ‘Kan Maciji’ Yana wanke tufafinsa duk da tsufarsa Baya ga wasu manyan hotuna biyu sai rajistar ta’aziyyar da aka jingine a…

  • Dalilin sa masa sunan ‘Kan Maciji’
  • Yana wanke tufafinsa duk da tsufarsa

Baya ga wasu manyan hotuna biyu sai rajistar ta’aziyyar da aka jingine a bangon gidan Pa Adama Aduku a garin Abejukolo na Karamar Hukumar Omala a Jihar Kogi, kusan za a iya cewa babu wani abu da zai nuna rasuwar tsohon sojan Najeriya da ya zama gwarzo a Yakin Duniya na Biyu.

“A gare shi, nuna alamun alhini ko kuma na sosa rai, alama ce ta ragwanci – wanda ba ya lamunta da haka,” inji wani daga cikin ’ya’yansa, Mista Oke Adama.

Sai dai lakabinsa ‘Kan Maciji’ na aika sakon firgici da kada hanta ga masu ziyarar gidansa. Yana kiran kansa da sunan “Oji ejo,” ma’ana “Kan Maciji” a harshensa na Igala. An yi imani cewa dafin maciji yana cikin kokon kansa inda yake harba shi ga duk abin da ya sara. Don haka, ga wannan dan mazan jiyan Yakin Duniyar, duk wani mahalukin da ya hantare shi shakka babu zai gamu da gamonsa daidai da yadda maciji yake harba dafinsa.

Sunan ‘Oji ejo’ da aka rika kiransa da shi a baya ya samo asali ne kan yadda yake bijire wa duk wani nau’in zalunci kyamarsa, kamar yadda Samuel Adama, daya daga cikin ’ya’yansa ya nuna. A wata hirar da ya yi da wata jarida ya ce wannan bijirewar tasa ce silar tunzura shi shiga aikin soja a daidai lokacin da bai ma taba tunanin yin haka ba. “Wata rana da maraice, kan hanyata ta dawowa gida daga gona, sai kawai na ga wani mutum  wanda na girme shi yana lakada wa mai garinmu duka. Mutumin mai suna Salikawa, soja ne ya yi ta dukan mai garin namu ne saboda mai garin ya ki dauka masa jakarsa don ya raka shi zuwa gidansa da ke nisan mil 10 da inda abin ya faru.

“Lokacin da aka gabatar da batun gaban DO na yankinmu, an umArci mai garin da lallai ya bi umarnin sojan, ko ya fuskanci duk wani hukunci da za a zartar a kansa, sakamakon turjiyar da ya nuna. Wannan abin ya dugunzuma ni sosai, inda daga nan kawai na ji lallai ne in shiga aikin soja; domin daga baya in koma kauyenmu da zimmar in lakada wa Salikawa dan karen duka saboda yadda ya wulakanta tare da cin zarafin mai garinmu,” Pa Aduku ya taba shaida wa jaridar Punch.

Ya kuma samu nasarar shiga aikin sojan: sai dai burinsa na ya koma kauyen da nufin ramuwar gayya kan cin zarafin mai garin nasu da Salikawa ya yi bai cimma nasara ba, saboda rasuwar Salikawa gabanin dawowar Pa Aduku daga Yakin Duniya.

Kamar dai yadda bayanan da iyalansa suka nuna, an haifi Pa Aduku a garin Odomagu, wani kauye da ke yankin Odo a Karamar Hukumar Omala a 1918, ya kuma shiga aikin soja a karkashin rundunar Royal West African Frontier Force a 1942, a Makurdi Jihar Binuwai. Bayanai sun ce, ya samu horon soja a Unguwar Shanu a Kaduna an kuma tura shi kasar Indiya lokacin Yakin Duniya na Biyu inda ya fafata a birnin Calcutta. Sa’annan ya ajiye aikin soja a 1946 bayan kammala Yakin Duniyar inda aka sallame shi a Legas, gabanin ya sake komawa ruwa a 1950 a Zariya. Sa’annan ya yi sake ajiye aiki na karshe a 1957.

Dansa ya bayyana yadda bayan barinsa mahaifinsu aikin soja lokacin da ya dawo daga Indiya ya taka sayyadarsa tun daga Apapa zuwa Ikeja lokacin da kusan duk birnin Legas yake dokar daji.

Bayan barinsa aikin soja na karshe, marigayin dan mazan jiyan ya zama dan kasuwa, inda ya yi ta safarar doya daga Lafiyar Barebari a Jihar Nasarawa ta yanzu zuwa garin Anacha. “A gaskiya na taso na iske shi yana wannan harkar  cikin shekaru gabanin ya dawo gida inda ya kama sana’ar noma gadan-gadan. Kwararren manomi ne; kuma ya yi suna wajen fara girbe doya kafin kowane manomi ya girbe doyarsa a duk fadin Karamar Hukumar Omala.

“Ya shiga siyasa. Jigo ne a Jam’iyyar NPN a Abejukolo, lokacin da yankin ya samar da Gwamna Aper Aku a 1979 da kuma Sule Iyaji a matsayin mamba a Majalisar Dokokin Jihar Binuwai, a 1979. Sa’o’insa a siyasa, su ne Alfa Okpanachi da James Omada Ita da Usman Akuta da Awodi Ashetu da kuma Oga Agege. Ya taka muhimmiyar rawa kuma jigo a majami’ar Abejukolo inda ya yi ayyuka da daman gaske ta fuskar ci gaban al’umma,” inji Samuel.

Hoton da marigayin ya xauka na karshe tare da iyalansa

Misis Pauline ta fada wa Aminiya cewa ya kamu da rashin lafiya a makon jiya. “Muna tunanin zazzabin maleriya ne ya kama shi sai dai kuma an yi masa magani har ya warke; amma jikinsa ya ta’azzara kwana biyu bayan haka. Don haka mun yanke shawarar kai shi asibitin Grimmad da ke Ayingba inda zazzabin ya yi ajalinsa,” inji ta. Ta ci gaba da cewa, duk da cewa ya sha miya sosai, amma ba su taba tunanin gajeriyar jinya za ta yi ajalinsa ba. “Yana da matukar wahala ka gan shi ya kwanta rashin lafiya duk da yawan shekarunsa. Yana nan da kwarinsa kuma ko sunkuyawa da tsofaffi ke yi; ba ya yi,” inji Pauline.

Daya daga cikin ’ya’yansa Misis Edna Adama, wacce ita ce ’yar autarsa mace, ta yi karin haske a kan koshin lafiya da tsabta da mahaifinsu ke da su. “Ba ya son kazanta ko kadan. Za ka gane haka da zarar ka gan shi ta hanyar la’akari da yadda yake sanya tufafi da yadda za ka tarar da dakinsa kullum a shiye tsaf-tsaf.

“Kullum za ka gan shi cikin fararen tufafi. Sannan da kansa yake wanke tufafinsa domin duk yadda za ka wanke masa ba zai gamsu ba. Kuma ko da ya amince ka taya shi wanki to daga baya sai ya sake wanke tufafinsa da kansa. Haka zalika dakinsa da kansa yake sharewa ya kuma gyara,” inji ta.

Ta ce daya daga cikin abincin da tsohon sojan yake matukar so shi ne shayi. Shi ne abin shansa a koyaushe. “Yana shan shayi kafin ya karya kumallo da bayan ya ci abincin rana haka abin yake idan zai ci abincin dare musamman koren ganyen shayi ba madara. A wasu lokutan abincin darensa shayi ne zalla; sannan yana yawan fada mana mu kasance muna shan shayi a koyaushe, yakan fada mana cewa duk wanda yake yawan shan shayi zai wahala ka ga yana fama da yawan rashin lafiya. Wadansu daga cikinmu sun koyi irin wannan al’ada ta shan shayi, kuma mun fahimci cewa yana kara koshin lafiya sosai,” inji ta.

 Waxansu daga cikin iyalan marigayi Pa Aduku
Waxansu daga cikin iyalan marigayi Pa Aduku

Shi kuwa Oke Adama cewa ya yi abin da yake burge shi da marigayin shi ne yadda yake nuna kauna ga ’ya’yansa da matansa. Koda yake dan mazan jiyan mabiyin addinin Kirista ne amma ya kasance yana da mata hudu da ’ya’ya 12 da jikoki 33. Dansa na fari, Mista Josiah Adama, an haife shi a 1949, dan autansa kuwa a maza an haife shi a 1984.

Oke ya ce, mun kasance kowa mahaifiyarsa daban amma ba ya nuna bambanci a tsakaninmu “Bai taba nuna wa wani daga cikin matansa ko ’ya’yansa bambanci ba. Wannan shi ne abin da ya kawo hadin kai a tsakaninmu. Sannan sai da ya tabbatar da dukkan iyalansa sun samu ilimi,” inji ta.

Edna, ta sake bayyana yadda mahaifinta yake nuna mata kauna, ta ce: “Wani lokacin shi zai hada min shayi sannan yana kawo mana tsaraba a duk lokacin da ya dawo daga tafiya. A lokacin da na gama Kwalejin Ilimi (COE) ta Jihar Kogi, sai ya saya mini babur saboda murnar na kammala karatuna lafiya, haka ya rika karfafa mana gwiwa da nuna mana kauna,” inji ta.

Daya daga cikin ’yar uwar tsohon sojan da ta rage a raye, Ageji Aduku, ta bayyana yadda yake nuna kauna ga ilahirin danginsa. Ta ce: “A lokacin da ya dawo daga yaki daga kasar Indiya ya kawo mini tsarabar sarka da dan kunne da sauransu. Duk da ina da aure, amma koyaushe ji yake yana da nauyi a kansa wajen kula da ni.”

Ta ce ta shiga cikin tashin hankali lokacin da ta ji an ce an kai dan uwanta asibiti inda daga bisani rai ya yi halinsa. “Zai yi wahala ka ga rashin lafiya ya kwantar da shi koda yake yakan yi fama da zazzabin maleriya da ciwon kai wani lokaci, amma da zarar ya sha shayinsa da maganinsa na gargajiya sai ya warware.

“Na umarci a kai ni wajensa. Ina so na ga halin da yake ciki, ana gobe zai rasu mun yi magana da shi ta waya. Ya ce mini kada in damu wajen zuwa duba shi. Ya ce mini shi zai zo gida ya duba ni da zarar an sallame shi. A ranar da ya ce mini zai zo gida domin in gan shi a ranar rai ya yi halinsa,” inji ta cikin kuka.

A halin yanzu iyalan marigayin suna ta shirye-shiyen bikin jana’izarsa koda yake har yanzu ba su fitar da sanarwar lokacin jana’izarsa ba.