✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Pakistan ta saki matar da ta yi wa addini batanci

A ranar Larabar da ta gabata ce aka tsaurara tsaro a Kasar Pakistan yayin da kotun kasar ke sakin matar nan da ta yi wa…

A ranar Larabar da ta gabata ce aka tsaurara tsaro a Kasar Pakistan yayin da kotun kasar ke sakin matar nan da ta yi wa addinin Islama batanci a shekarar 2010.

An dai baza jami’an tsaro a manyan biranen kasar, a kokarin dakile duk wani yunkurin kai hare-hare daga masu kaifin kishin addini, yayin da kotun ta sallami matar wacce bin addinin Kirista, mai suna Asia Bibi, wadda da ma aka yanke wa hukunci saboda batanci da ta yi wa addinin na Islama.

Bayanan da ke fitowa daga Islamabad babban birnin kasar, sun tabbatar da ganin wasu zaratan jami’an tsaron cikin shirin ko-ta-kwana, a wasu muhimman gine-ginen gwamnati, yayin da a gefe guda kuma masu kishin na addini suka ja damara.

Haka nan hukumomin birnin Lahore sun gayyato sojoji bayan samun rahotannin kungiyar nan ta Tehreek-e-Labaik, na yunkurin kutsawa majalisar dokokin yankin. A kudancin birnin Karachi ma, an ce wasu iyayen na gaggawar zuwa makarantu don kwaso ‘ya’yansu saboda irin fargabar da ake ciki na yiwuwar tada husuma.