✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Paul Biya: Shugaban Kamaru tun 1982 ya sake lashe zabe

Shugaban Kamaru Mista Paul Biya mai shekara 85 a duniya wanda ya fara mulkin kasar tun a 1982 kimanin shekara 36, ya sake lashe zaben…

Shugaban Kamaru Mista Paul Biya mai shekara 85 a duniya wanda ya fara mulkin kasar tun a 1982 kimanin shekara 36, ya sake lashe zaben Shugaban Kasar karo na bakwai.

Paul Biya dai yanzu shi ne Shugaban Kasar da ya fi tsufa a Afirka, kuma ya lashe zaben ne da kashi 71.3 cikin 100 na kuri’un kamar yadda BBC ya ruwaito sakamakon zaben daga hukumar zabe.

A zaben wanda mutane da dama ba su fita kada kuri’a ba, kuma yake cike da tsangwamar masu kada kuri’a, an girke ‘’yan sandan kwantar da tarzoma a manyan biranen Yaounde da Douala cikin shirin ko-ta-kwana saboda zanga-zangar ’yan adawa.

An shafe fiye da shekara guda ana rikici a yankunan da ke amfani da Ingilishi da kuma hare-haren ’yan aware da suka yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.

Kwanaki biyu kafin a saki sakamakon zaben, Shugaban Ekuatorial Guinea da ke makwabtaka da Kamarun wanda ya fi kowa dadewa a karagar mulki cikin shugabannin Afirka, Teodoro Obiang Nguema ya taya Mista Biya murna kan nasarar da ya yi.

Maurice Kamto na Jam’iyyar MRC/CRM, ya samu kashi 14.2 cikin 100. Amma a birnin Doula Mista Kamto ya buge Mista Biya da rata mara yawa.

A fadin kasar kuwa, rabin mutanen da shekarunsu suka kai su kada kuri’a ne kawai suka yi zaben.

Dubban mutane ba su samu damar kada kuri’a ba saboda matsalar rashin tsaro yawanci saboda barazanar barkewar rikici da ’yan tawaye ke yi.

A ranar zabe kuwa dakarun tsaro sun harbe wadansu ’yan aware uku da ake zargi da bude wa masu wucewa wuta.

Wadansu ’yan tawaye sun yi kokarin kawo tarnaki ga rabon kayan zabe inda suka haramta yin tafiya baki daya.

Kashi biyar cikin 100 ne kawai suka kada kuri’a a yankuna biyu da ke amfani da Ingilishi, a cewar Kungiyar Magance Rikici ta Duniya kamar yadda BBC ya jiyo.

Alkaluman hukumomi sun nuna cewa kashi 16 cikin 100 ne suka fita zaben a yankin masu amfani da Ingilishi a Kudu maso Yammacin kasar.

Shaidu sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa sun ji karar harbe-harbe a ranar Litinin da safe a Buea, babban birnin yankin masu Ingilishi da ke Kudu maso Yamma.

’Yan adawa sun shigar da kusan korafe-korafe 18 da aka yi na zaben don yin zagaye na biyu, inda wadansu ke zargin an yi zamba a Kotun Tsarin Mulki ta Kamaru, hukumar da ke da alhakin sanar da sakamakon, tun kafin ma a saki sakamakon.

Daga cikin masu kira da a sake sabon zabe har da manyan abokan karawar Mista Biya – Mista Kamto da Joshua Osih na jam’iyyar adawa ta SDF/FSD.

A kwanakin baya Aminiya ta ruwaito cewa an shiga rudani  game da sakamakon zaben kasar bayan Mista Kamto ya ayyana kansa a mastayin wanda ya lashe zaben duk da cewa a lokacin hukumar ba ta fitar da sakamako ba, wanda har ta gargade shi.

Masu sa ido daga Kungiyar Tarayyar Afirka sun ruwaito cewa an yi zaben lafiya, amma sun kara da cewa “Mafi yawancin jam’iyyun ba su da wakilai” a batun wadanda ake bari su lura da yadda ake kada kuri’a da kuma kirga kuri’un a rumfunan zabe.

Kungiyar da ita kadai ce ta tura masu sa ido ita ce Kungiyar Kasashe Rainon Faransa, wadda shugabanta ya bukaci masu ruwa-da-tsaki da ’yan takara su yi bakin kokarinsu wajen ganin an yi komai lafiya, su kuma yi amfani da hanyoyin da shari’a ta tanada don kalubalantar sakamakon.