✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Paulinho ya barke da kuka jim kadan da sanya hannu a kulob din Tottenham

dan wasan tsakiya da ya buga wa kasar haihuwarsa Brazil a gasar cin kofin zakarun Nahiyoyi (Confederations Cup) da aka kammala a karshen makon jiya,…

dan wasan tsakiya da ya buga wa kasar haihuwarsa Brazil a gasar cin kofin zakarun Nahiyoyi (Confederations Cup) da aka kammala a karshen makon jiya, kuma dan kwallon Corinthians da ke kasar, a ranar Talatar da ta wuce ne ya canja sheka zuwa kulob din Tottenham da ke Ingila.
Kulob din na Tottenham ya saye shi ne a kan Fam miliyan 17.
Kafar sadarwar Sportsmail a makon jiya ta kalato cewa akwai yiwuwar dan kwallon ya canza zuwa Ingila da zarar an kammala gasar cin kofin zakarun nahiyoyi don haka yanzu za a iya cewa zancen ya zama gaskiya.
Paulinho, wanda ya barke da kuka a lokacin da yake ban kwana da magoya bayan kulob din Corinthians, ya bayyana juyayin rabuwa da su ne a lokacin da ya saba da su inda ya yi musu fatan alheri.
“Abin da nake so na fada ga magoya baya da mahukunta kulob din Corinthians shi ne zan yi rashin ku kuma ina fata mu sake haduwa nan gaba, don haka ina godiya da hadin kai da goyon bayan da kuka nuna mini a daukacin zaman da na yi a wannan kulob”, inji Paulinho a lokacin da yake sharbar kuka.
Babban Daraktan da ke kula da harkokin kwallo a kulob din, Roberto de Andrade ya yaba wa dan kwallon musamman kasancewarsa daya daga cikin ’yan kwallon da suka taimaki Brazil wajen lashe kofin zakarun nahiyoyi da ya gudana a kasar bayan kasar ta lallasa Sifen da ci 3-0 a wasan karshe.