Notice: Undefined index: show_thumbnails in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 199

Notice: Undefined index: show_headline in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 200
PDP ba za ta sake tasiri a Jihar Kaduna ba – El-Rufa’i - Aminiya
Aminiya

PDP ba za ta sake tasiri a Jihar Kaduna ba – El-Rufa’i

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya  ce Jam’iyyar PDP ba za ta sake yin tasiri a jihar  ba.

Gwamna El-Rufa’i ya ce Jam’iyyar PDP a shekara 16 da ta yi a mulkin jihar babu abin da za ta nuna a jihar in ba Titin Kawo mai doro daya ba.

Gwamna ya bayyana haka ne okacin da ya karbi bakuncin wadansu ’ya’yan Jam’iyyar APC da suka kai masa ziyara domin taya shi murnar tabbatar masa da kujerarsa da Kotun Kararrarakin Zabe ta yi.

Ya kara da cewa kotun ta nuna cewa masu gaskiya ne, suke da gaskiya, yayin da masu karya aka tabbatar musu da cewa su makaryata ne.

“In Allah Ya yarda PDP ba za ta sake yin tasiri a Jihar Kaduna ba. Ba mu son cika yin magana domin idan Allah Ya ba ka shugabanci abin da ya kamata ka yi shi ne mayar da hankali wajen yi wa mutane aiki,” inji El-Rufa’i.

ADVERTISEMENT

Ya ce baya cika son yin magana a kan batun almundahana da kudi da suka yi a lokacin mulkinsu.