Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

PDP da APC sun sa zare kan Shugabancin Majalisa

PDP da APC sun sa zare kan Shugabancin Majalisa

Cacar baki ta barke a tsakanin Jam’iyyar PDP mai adawa da Jam’iyyar APC mai mulki, bayan APC ta ba ’ya’yanta umarnin su zabi shugabannin Majalisar  Dokoki ta Kasa daga cikinsu, tare da ayyana goyon baya ga wadanda take so a zaba.

Sai dai Jam’iyyar PDP ta kalubanci wannan umarnin, inda ta bukaci ’ya’yanta su yi takarar kowane mukami da ke majalisar.

ADVERTISEMENT

A shekarar 2015, Jam’iyyar PDP ta shammaci APC inda danta ya samu kujerar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.

Kuma mukaman Shugaban Majalisar Dattawa da na wakilai suka fada hannun wadanda jam’iyyar ta ce ba su kwanta mata ba domin ba su ta tsayar ba.

ADVERTISEMENT

PDP ta ce babu wata doka da ta hana ’ya’yanta neman shugabancin majalisun biyu da na muhimman kwamitoci.

Sakataren Jam’iyyar PDP Sanata Umaru Tsauri ya ce tsarin mulkin Najeriya bai ce “dole sai wane, ko wane ba.”

Sai dai Sakataren Walwala na Jam’iyyar APC Alhaji Ibrahim Masari ya ce har yanzu suna kan bakarsu kamar yadda BBC ya ruwaito.

“Wanda duk yake da rinjaye shi ne zai zama Shugaban Majalisar Dattawa da kuma Majalisar Wakilai,” inji shi.

Jam’iyyar APC ta kebe shugabancin Majalisar Dattawa ga Shiyyar Arewa maso Gabas tare da bayyana sunan wanda take so ya kasance shugaba.

Sanata Ahmed Lawan daga Jihar Yobe ne jam’iyyar ta zaba a matsayin wanda take son ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.

APC ta ce ta yanke wannan hukunci ne na zabar Sanata Ahmad Lawan ya jagoranci Majalisar Dattawa da yawun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da manyan jiga-jiganta.

Amma batun shugabancin majalisun na neman zame wa Jam’iyyar APC da wadansu ’ya’yanta alakakai.

Wadansu daga cikin ’yan majalisar sun ce hakan ba adalci ba ne, kamata ya yi a bar masu son mukaman su yi takara, amma jam’iyyar ta ce ba za ta sauya matsayinta ba.

Majiyoyi sun ambato Sanata Ali Ndume daga Arewa maso Gabas yana adawa da zabin uwar jam’iyyar, inda ya ce kamata ya yi a bar sanatocin shiyyar su baje a faifai maimakon jam’iyyar ta nuna inda ta karkata.

Masu sharhi suna ganin wannan matakin na Jam’iyyar APC zai jawo mata matsala idan ba a yi kokarin sulhu cikin sauri ba.

Farfesa Jibril Ibrahim na Cibiyar Bunkasa Dimokuradiyya a Najeriya ya ce ana iya shiga rikici tun kafin a fara aiki a majalisar.

Ya ce ’ya’yan jam’iyyar za su iya rabuwa kashi biyu, wadansu su goyi bayan zabin jam’iyyar wadansu kuma su bijire su zabi wani dan takarar.

A bangaren Majalisar Wakilai kuwa, Honorabul Gudaji Kazaure wanda shi ma ya nuna sha’awarsa ta neman kujerar Shugaban Majalisar Wakilai ya nuna ba ya goyon bayan kebe mukami ga wata shiyya illa a baje a faifai mai rabo ya samu.

Dan majalisar ya shaida wa BBC cewa yana nan kan bakarsa ta neman kujerar kuma zai nemi goyon baya daga ’yan uwansa ’yan majalisa domin su zabe shi.

Gudaji Kazaure ya ce ya ja kunnen APC cewa idan ba a yi hattara ba abin da ya faru a 2015 yana iya sake faruwa a bana.

Ya yi kira ga Shugaban Kasa Buhari ya diba magoya bayansa irinsa wadanda ba za su bari a saba masa ba.

“Ba yadda za a yi a ce an ci yaki an yi nasara amma idan an zo kason ganima a ce ba za a fara duba wadanda suka fi shan wahala da yin biyayya ba,” in ji shi.

Ya kara cewa ya kamata a duba a ga wadanda suka fi jajircewa a ba su shugabancin majalisa.

A ba ni Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ko in nemi shugabancinta- Orji Kalu

A nasa bangaren, zababben Sanata mai wakiltar Arewacin Abiya, kuma tsohon Gwamnan Jihar Abiya Cif Orji Uzor Kalu wanda ya lashe zabe a Jam’iyyar APC ya ce ko dai a bar masa kujerar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, ko kuma ya tsaya takarar kujerar shugaban domin ya kamata yankinsa na Kudu maso Gabas su samu wakilci.

Ya ce zai amince da tsarin Jam’iyyar APC na ba yankin Arewa maso Gabas Shugaban Majalisar, amma ya bukaci a yi wa yankinsa adalci.