✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP na shirin dakatar da Jonathan kan faduwarta a  zaben Bayelsa

Mai yiwuwa Jam’iyyar PDP ta dakatar da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan daga cikinta bisa zargin ya tallafa  Jam’iyyar APC, wanda hakan ya taimaka…

Mai yiwuwa Jam’iyyar PDP ta dakatar da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan daga cikinta bisa zargin ya tallafa  Jam’iyyar APC, wanda hakan ya taimaka wajen kayar da jam’iyyarsa a zaben Asabar da ta gabata a  jiharsa ta Bayelsa.

Dan takarar Jam’iyyar APC Dabid Lyon ya samu kuri’a dubu 352 da 552, inda ya kayar da dan takarar Jam’iyyar PDP, Mista Duoye Diri wanda ya samu kuri’a dubu 143 da172.

Ga  wadansu jiga-jigan PDP rasa jihar ga APC bayan shekara 20 PDP tana juya jihar ya faru ne saboda halin ko-n-kula da Jonathan ya nuna kan abin da zai iya faruwa da jam’iyyar a lokacin zaben.

Manyan ’ya’yan jam’iyyar da suka tattauna da Aminiya ranar Litinin sun koka kan mugun rawar da jam’iyyar ta taka a zaben aka kammala inda suka nemi a yi bincike.

Kasancewar tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan babban jigo a Jam’iyyar PDP ya kara sa jama’a suna tambaya kan nasarar da Jam’iyyar APC ta samu a jihar.

Sakamakon ya nuna irin girman tazarar da APC ta bai wa PDP, inda ta rubanya ta sau fiye da biyu.

Yanzu dai Jihar Bayelsa ce ta biyu a yankin Neja Delta da Jam’iyyar APC mai mulki ta karbe daga PDP.

Shin APC ta mamaye Bayelsa?

Tambayar da ke bakunan jama’a ke nan. Sai dai masu lura da al’amura irin su Dokta El-Haroon Muhammad na Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Tarayya da ke Kaduna na ganin ba haka al’amarin yake ba.

El-Haroon ya ce zai yi wuya duk da cewa Jam’iyyar APC ke da madafun iko a tarayya, ta iya yi wa Jam’iyyar PDP irin hawan kawarar da ta yi mata a jihar, ba tare da wata makarkashiya daga cikin gida ba.

“Da ma ita siyasa kulle-kulle ce. Ita siyasa makirci ce,” inji shi

Ruwa ba ya tsami banza

Sakamakon zaben Bayelsa ya nuna Dabid Lyon na jam’iyyar APC ya ci kananan hukumomi shida daga cikin takwas, ciki har da Karamar Hukumar Ogbia ta tsohon Shugaban Kasa Jonathan.

Koda a Otouke garin su  Jonathan Jam’iyyar APC ce ta yi nasara a kan PDP.

Bisa la’akari da farin jini da karfin fada-a-ji da tsohon Shugaban Kasar yake da su a mahaifarsa da sauran sassan jihar, wadansu na ganin idan dai ba ya ba da kofa ba, to da wuya a yi wa jamiyyar irin wannan hawan kawara.

Rahotanni na alakanta rashin nasarar Jam’iyyar PDP da rashin jituwa a tsakanin Gwamna mai barin gado, Seriake Henry Dickson da Mista Jonathan.

An ce rikici a tsakanin mutum biyun ya samo asali ne tun daga zaben wanda Jam’iyyar PDP za ta tsayar takarar Gwamna.

El-Haroon Muhammad yana ganin “Bakin jinin da Gwamna Seriaki Dikson ke da shi ka iya zama dalilin faduwar PDP.

Ya  ce “Akwai yiwuwar shi ma Jonathan ya bi sahun mai dakinsa, Dame Patience wadda ta fito kiri-kiri ta ce APC za ta zaba.”

To sai dai wadansu masu lura da al’amura na ganin Jonathan ya sakankance da harkar siyasa tun bayan da ya sha kaye a zaben shekarar 2015.

Me ya kai shugabannin APC wurin Jonathan?

Rahotanni sun ce a ranar Lahadi ce wani ayarin shugabannin Jam’iyyar APC a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammadu Badaru suka kai ziyara gidan Mista Jonathan a garin Otouke.

Wani dan Jam’iyyar APC, Ileowo Kikiowo ya ce Gwamna Badaru wanda shi ne jagoran yakin neman zaben Jam’iyyar APC a zaben Gwamnan Jihar Bayelsa da Sanata Itang Enang sun ziyarci Goodluck Jonathan.

Wannan ziyara dai ta faru ne a daidai lokacin da jama’ar jihar ke cikin rudu kan mutumin da Jonathan zai mara wa baya kasancewar shi da Seriaki Dickson sun raba-gari.

To sai dai Jonathan ya musanta rade-radin da ake yi cewa ya yaki jam’iyyarsa ta PDP a zaben Gwamnan jiharsa.

Ziyarar Jonathan ga Buhari

Tun bayan karbar mulki daga hannun Jonathan, ba a taba jin wata mummunar kalma ta fito daga bakin Shugaba Buhari kan Jonathan din ba, duk da cewa Gwamnatin Buhari ta sha nuna wa tsohuwar gwamnatin yatsa kan wasu tuhume-tuhume.

Sai dai a wasu lokutan baya, Shugaba Jonathan ya sha yin hannunka mai sanda ga gwamnatin Buhari duk da cewa shi ma bai taba kama suna ba.

To amma a baya-bayan ne Shugaba Buhari ya yi wata ganawa da Jonathan a fadar gwamnati da ke Abuja. Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya sanar da haka a shafinsa na Twitter cewa Shugaban ya karbi bakuncin Jonathan a fadar gwamnati, sai dai bai fayyace dalilin ganawar ba. Jonathan da Buhari dai sun kasance cikin sakin fuska da walwala yayin ziyarar.

El-Haroon ya ce “Rade-radin da ake yi shi ne Jonathan zai koma Jam’iyyar APC a Jihar Bayelsa.” Ya kara da cewa bisa la’akari da yadda siyasar Najeriya ta bambanta da ta sauran kasashen duniya, babu mamaki idan wani tsohon Shugaban Kasa ya koma jam’iyyar Shugaban da ya kayar da shi,” inji shi.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne yadda zababben Gwamnan Jihar Bayelsa zai tafiyar da mulki  tare da majalisa mai cike da rinjayen ’ya’yan PDP da kuma irin yadda alaka za ta kasance tsakaninsa da Shugaba Jonathan.

Buhari ya taya Yahaya Bello da Dabid Lyon murnar lashe zabe

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya Yahaya Bello murnar lashe zaben Gwamnan Jihar Kogi. Shugaban Kasar ya bayyana zaben da nasarar dan takarar Jam’iyyar APC a matsayin nasara mai kyau. “Ya yaba wa magoya bayan APC kan jajircewar da suka yi da tsayawa tsayin-daka duk da rikice-rikicen da aka fuskanta.

Hakazalika Shugaban ya mika sakon taya murna ga sabon Gwamnan Jihar Bayelsa Dabid Lyon. A takardar da aka raba wa manema labarai wadda Kakakin Shugaban Kasa Femi Adesina ya saka wa hannu, Shugaba Buhari ya yi kiran a rika kai zuciya nesa a lokutan zabe a daina yawan tada husuma. Ya ce irin haka nuni ne cewa lallai akwai sauran gyara da za a yi nan gaba domin a rika samun zabe mai tsabta. Sannan ya mika ta’aziyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a lokacin zaben.

Bayan nan ya yaba wa hukumar zabe bisa namijin kokari da ta yi wajen gudanar da zabubbukan. Sai ya yi kira ga zababben Gwamnan Bayelsa Lyon ya rike jama’arsa da kyau sannan ya rungumi kowa, ya kuma yi wa jihar Bayelsa ayyuka nagari don ci gaban al’ummar jihar.