Da Dumi Dumi

PDP na so Kotun Koli ta sake duba zaben Shugaban Kasa

Jam’iyyar PDP ta ce za ta bukaci Kotun Koli ta sake duba hukuncin da ta yanke kan zaben Shugaban Kasa inda ta tabbatar da nasarar Shugaba Buhari a zaben bara.

Da yake magana a wani taron manema labarai da jam’iyyar ta kira a ranar Litinin a Abuja, Sakatare Watsa Labarai na Jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ya ce jam’iyyar ta kuma shirya don bukatar Kotun Kolin ta sake duba hukuncin da ta yanke kan zabubbukan gwamnonin jihohin Katsina da Kano da Kaduna.

Ya ce “Jam’iyyar PDP ta yi Allah wadai da yunkurin Jam’iyyar APC na kokarin yi wa hukuncin Kotun Koli kan zabubbukan gwamnonin Bayelsa da Zamfara karan-tsaye.” Don haka masu ruwa-da-tsaki na Jam’iyyar PDP sun yanke shawarar neman Kotun Kolin ta sake duba batun da suka gabatar kan takardun bogi da dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar APC ya yi.

“Haka kuma abin yake game da zaben Gwamnan Jihar Katsina inda lauyoyinmu suka gabatar da zargin gabatar da takardun bogi da Gwamnan Jihar na APC ya yi. Don haka PDP ba ta da wani zabi illa ta nemi Kotun Koli ta sake duba hukuncin zaben gwamnonin Kaduna da Kano da  Katsina,” inji shi.

 

ADVERTISEMENT

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya