✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta caccaki Buhari kan hari a ofishin Najeriya da ke Ghana

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kalubalanci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya farka ya magance matsalar diflomasiyyar da Najeriya ke fuskata ta kai hare-hare…

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kalubalanci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya farka ya magance matsalar diflomasiyyar da Najeriya ke fuskata ta kai hare-hare kan ‘yan kasar da ke zaune a kasashen waje.

Jam’iyyar ta bukaci shugaban da ya dauki tsatstsauran mataki musamman kan rushe ofishin jakadancin Najeriya da ke Ghana, wanda ta bayyana a matsayin raini.

Rahotanni dai sun nuna cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ce wasu fusatattun matasa dauke da makamai suka far wa ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin Accra na kasar Ghana suka kuma rusa wani sashe da ake kan ginawa a ofishin. Sashen dai ana gina shi ne don ya zama masaukin ma’aikatan ofishin da kuma baki.

Gabanin haka wani hamshakin dan kasuwa a kasar ne dai ya zargi ofishin jakadancin da yin kutse kan filinsa.

To sai dai jam’iyyar PDP a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin mai dauke da sa hannun Sakataren Yada Labaranta na Kasa, Kola Ologbondiyan ta ce hakan ta faru ne sakamakon wasarere da raunin shugabancin gwamnati mai ci wajen kare martabar Najeriya a idanun duniya.

“PDP tana takaici da kuma Allah-wadai cewa tun da lamarin ya faru, Shugaba Buhari da jam’iyyarsa ba su yi wani hobbasa ba wajen kare martabar kasar in ban da wata sanarwar da Ministan Harkokin Kasashen Waje Geoffrey Onyeama ya fitar.

“Kazalika PDP ta tuno karara yadda shugaban ya gaza yin abin da ya dace lokacin da aka rika kai wa ‘yan Najeriya hare-haren kin jinin baki a Afirka ta Kudu”, inji sanarwar.