✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta fara laluben dan takarar Shugaban kasa a 2019

Shugaban Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP ta kasa, Sanata Walid Jibrin, ya ce jam’iyyarsu ta fara laluben wanda za ta tsayar a matsayin dan takararta…

Shugaban Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP ta kasa, Sanata Walid Jibrin, ya ce jam’iyyarsu ta fara laluben wanda za ta tsayar a matsayin dan takararta a zaben Shugaban kasa na shekarar 2019.

Sanata Jibrin ya kuma nanata  fatan da suke da shi cewa wadansu ’ya’yan jam’iyyar da a yanzu ke cikin APC, za su dawo cikin jam’iyyarsu ta asali wato PDP nan ba da jimawa ba.

Sanata Jibrin ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake karbar bakuncin wata tawagar kungiyar wakilan mazabu da suka kai ziyara ofishinsa da ke Abuja. Ya kara da cewa wadanda suka fice daga PDP a shekarar 2015, duk za su dawo gida nan ba da dadewa ba.

Kuma ya bayyana tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin mutumin kirki kuma gogaggen dan siyasa. Shugaban Kwamitin Amintattun na PDP, ya ce daga cikin wadanda ake sa ran dawowarsu PDP akwai Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Tambuwal da sauransu.

Ya ce, “Ba mu da wani rikici a jam’iyyarmu ta PDP, saboda dukanmu mun amince daga Arewa PDP za ta tsaida dan takarar Shugaban kasa a zaben 2019. Don haka ina rokon ku mara wa dan takarar Arewa baya domin ku samu shugabancin da ya cancanta. Muna yin iyakar kokarinmu don ganin an tsaida dan takara daga Arewa wanda ya fi cancanta ya shugabanci Najeriya, da zai iya kwace mulki daga Jam’iyyar APC. Saboda shekarar 2019 tamu ce.