✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta mutu tana jiran binnewa ne kawai – Liman kaura

Sakamakon hade wasu jam’iyyun siyasa don ta da sabuwar Jam’iyyar APC, wasu ’yan siyasa na murna ne wasu na bakin ciki saboda rasa kujerunsu. Wakilinmu…

Bashir  Liman KauraSakamakon hade wasu jam’iyyun siyasa don ta da sabuwar Jam’iyyar APC, wasu ’yan siyasa na murna ne wasu na bakin ciki saboda rasa kujerunsu. Wakilinmu ya nemi jin ta bakin wani matashin dan siyasa don jin ko mene ne ra’ayinsa kan wannan hali da suka tsinci kansu a ciki:

Aminiya: Mene ne sunanka kuma mene ne mukaminka a Jam’iyyar ANPP da aka rushe a yanzu?
Liman: Sunana Bashir Sahabi Liman daga kauran Namoda na ke, kuma ni ne Sakataren Jam’iyyar ANPP a karamar Hukumar kauran Namoda a Jihar Zamfara, kuma ina cikin masu ba Gwamna shawara kan harkar zakka da wakafi, a shugabanci na siyasa an sauke mu kamar yadda ka sani, muna sauraren inda Ubangiji zai ajiye mu.
Aminiya: To ga shi yanzu kun koma Jam’iyyar APC me za ka iya cewa?
Liman: Babu abin ya fi sai dai mu yi godiya, kuma abin farin ciki ne, saboda an yi haka ne domin a kawo gyara, a fidda kasar nan cikin halin da muka tsinci kanmu a ciki na wahala. Idan na ce mawuyacin hali ba sai na yi dogon bayani ba, domin kowa ya san jama’a sun shiga halin lahaula. Kuma idan ka dubi wadanda suka shirya wannan hadaka ka san sun san abin da suke yi kuma tsofaffin ’yan siyasa ne, za mu bi su don mu taimaka masu. Ka san wani lokaci Hausawa suna cewa ba a mugun sarki sai mugun bafade, da yawa mataimaka suke lalata abubuwa, suke bi-ta-da kulli ga duk wani shiri don kada a ci nasara.
Aminiya: Wasu suna ganin a yayin da wasunku ke murna wasu bakin ciki suke yi domin an sauke su daga kan kujerunsu, me za ka ce?
Liman: Babu shakka abin bai yi wa wasu dadi ba, domin sun rasa damar da suke da ita. Wasu  asirinsu ya tono babu maganar cuta, babu cin amana sai dai su koma gefe su yi kallo, domin wasu sun san a nan Jihar Zamfara ba za a yi tafiya da su ba, saboda an san macuta ne, shi kansa Gwamna ya san macuta ne ya kyale su ne da halinsu sai yanzu da lokaci ya zo. Gwamna yana bakin kokarinsa, amma ya gamu da mugayen mutane da mugayen masu hassada, saboda duk wanda ya zo Jihar Zamfara ya san an samu canji, dubi hanyar kaura zuwa Zurmi, yanzu za ka iya zuwa Katsina a kanta. Na biyu dubi asibitoci da muke da su su ma ba a magana a dubi harkar noma har a daminan bana taki Naira dubu daya aka saida mana da sauransu, amma duk da haka su macutan ne ke zaginsa. Idan wannan aikin aka shekara hudu ana yi me kake tsammani a cikin shekara takwas. Don haka mu muna cikin murna saboda mun san ba mu cuci kowa ba kuma ba mu yi wa kowa hassada ba.
Aminiya: Kana ganin da wannan hadaka Jam’iyyar APC za ta iya kwace mulki daga PDP?
Liman: Ka kurkure bakinka don tambayarka ba ta da tsarki, ai PDP a yanzu ta mutu murus tana jirar binnewa ne kawai. Ba ka ga yadda suka dage suna fada da junansu ba, kuma ba ka ji Gwamna Abdul’aziz Yari ya ce lokaci muke jira mu fatattaki PDP a kasar nan ba, in Allah Ya yarda ta bar mulki ta gama, kuma su wane ne a PDP yanzu duk an bar ta ba ka ji Atiku ba ne ba ka ji Babangida ba ne, ba ka ji Sule Lamido da Kwankwaso da Nyako da sauran manyan PDP da jam’iyyar take ji da su ba ne? aAi lokaci ne ya yi kowa ya gaji, ba su da wani farin jini a yanzu, abin da ya faru a nan Jihar Zamfara shi ne zai faru a kasar nan. Idan ba ka manta ba, ita ke mulki a nan jihar, kuma a kullum sai su nuna su ne suke da kudi da mulki, mu kuwa ba mu da komai sai Sanata Ahmad Sani da Mai daraja Gwamna, suka rika cewa mu yawaita Ina lillahi wa’inna ilaihi raji’un mu rika karantawa a kullum da abin ya yi tsanani zai yi sauki, kuma kowa ya ga sakamako, wannan nasara ce daga Allah Mai kowa Mai komai, don haka mun sanya Allah a gaba.
Aminiya: An ce ku matasa da ku ake amfani, ana bangar siyasa ana kashe wasu a kona gidajen wasu, me za ka ce?
Liman: Dole matasa su ajiye bangar siyasa su zama mutane, ya zama suna cin gajiyar abin da suka aikata na siyasa, a rika ba su mukamai ana ba su aiki. Yanzu idan ka dubi matasan Zamfara dole ka yaba da yawa an ba su aiki, an ba su mukamai an ba su babura da mutoci don su ci abinci. Mun san ba kowane matashi ne zai samu aikin yi ba, amma idan aka ba wasu abin sana’a dole su amfana su kuma ciyar da wasu, ba ka ganin yadda Gwamman ya dauki wannan mataki ya sa yanzu an samu saukin matasa masu bi ofisoshi suna hana ma’aikata aiki, wasu suna tumasanci a gari, don haka kada wani dan siyasa ya dauka abin kamar da yake, babu wanda zai yi amfani da matasa su kashe wani ko su kona gidan wani su ma mutane ne suna ci suna sha suna da iyali , wasu suna da digiri.
Aminiya: Wace shawara za ka ba sababbin shugabannin sabuwar jam’iyarku ta APC?
Liman: Shawarata gare su ita ce a ji tsoron Allah. Su tuna ba kowa ne zai samu mukami ba, su zama mutanen kirki ba domin sun fi saura aka ba su ba, don haka su rike mutane da amana, kada suce ai wane ba dan tsohuwar jam’iyyarmu ba ne, sai wanda muke tare zan ba wani abu ko mukami.