✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta yi tir da hari kan mambobinta a Sakkwato

  Jam’iyyar PDP ta yi tir da harin da matasa ‘yan bangar siyasa suka kai wa mambobinta a Jihar Sakkwato kwanan nan. Wuraren da aka…

 

Jam’iyyar PDP ta yi tir da harin da matasa ‘yan bangar siyasa suka kai wa mambobinta a Jihar Sakkwato kwanan nan.

Wuraren da aka kai harin sun hada da gidan Tsohon Kwamishinan Harkokin Addini, Alhaji Abdullahi Maigwandu inda aka farfasa gilashin gaba da baya na  motocin gidansa da na tsohuwar ma’aikatarsa guda 7, sai karamin ofis na kamfen din Tambuwal dake kan titin Sarki Yahaya da suka kare allon hutunansa.

Haka kuma an kai hari gidan Almustafa Alhazai, inda aka shiga shagon sayar da wayoyin hannu dake makale da gidan aka kwashe wayoyin da kudinsu ya kai dubu 600. Harin ya kuma shafi ofishin kamfen na Atiku Abubakar, inda aka farfasa gilashin motar da ke wurin tare da bata allunan siyasa. A sanarwar da jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar, Alhaji Abdullahi Hausawa ya fitar ya zargi Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da daukar nauyin bata garin su yi wannan aika-aikar.

“Ya kamata Sanata Wamakko ya sanya kansa cikin mutane masu mutunci da son zaman lafiya a jiha, amma ba daukar matakin muzgunawa da cin zarafin jama’a da wasa da dukiya da rayuwar al’umma ba,” a cewarsa.

Hausawa, ya kuma yi kira ga ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar Sakkwato da su shiga cikin lamarin dan kwatowa masu hakki hakkinsu.

A martaninsa, Shugaban APC na Sakkwato, Alhaji Isah SadiK Acida ya ce jam’iyyarsu ba su san da wannan ba, rigima ce ta tsakanin bangarori biyu, ba ruwansu da wannan. Ya ce rigima ce tsakanin bangaren tsohon gwamna Attahiru Bafarwa da Gwamna Aminu Tambuwal, amma suka sanya Wamakko ciki don su boye lamarin.

Jami’ar hulda da jama’a ta hukumar ‘yan sanda, Cordelia Nwewe ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce ‘yan sanda na kan bincike.