✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta zargi APC da kawo mata hargitsi lokacin kamfenta a Kano

Jam’iyyar PDP a Jihar Kano ta dora alhakin  hargitsin da ya tashi a lokacin da jam’iyyar ta gudanar da kamfe a Karamar Hukumar Birni da…

Jam’iyyar PDP a Jihar Kano ta dora alhakin  hargitsin da ya tashi a lokacin da jam’iyyar ta gudanar da kamfe a Karamar Hukumar Birni da Kewaye a kan Jam’iyyar APC, inda ta ce APC ta yi hayar matasan da suka yi basaja a cikin taron nasu tare da kai hare-hare kan ’ya’yan jam’iyyar na hakika. Wannan bayani ya fito daga bakin Mataimakin Dan takarar Gwamnan na Jam’iyyar PDP Kwamared Aminu Abdussalam a wajen taron da ya yi da manema labarai a shekaranjiya Laraba.

Kwamared Abdussalam ya ce kasancewar suna gudanar da tarurrukansu lafiya lau hakan ya sanya har mata masu shayarwa ke halarta. “Kowa ya san tun daga lokacin da muka fara yakin neman zabe lafiya lau muke yi. Mun gudanar da kamfen a kananan hukumomi 37 amma babu inda aka ji wani abin Allah-wadai ya auku. A tarurrukanmu za ku tarar har da mata masu shayarwa saboda gamsuwa da suka yi ba mu harka da makamai,” inji shi.

Ya ce ganin dimbin jama’ar da ke fitowa lokutan tarurrukansu ya sa Jam’iyyar APC ta dimauce har ta kai ga aikata abin da ta aikata kwanaki kadan bayan jam’iyyun sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar gudanar da kamfe da kuma zabe lafiya. “Mun kama mutum biyu daga cikin wadanda suka jawo mana wancan hargitsi tare da mika su ga hukuma. A lokacin da muke bincike ne muka gano cewa matasa ne da aka yi hayar su don kawai su bata mana suna su kuma zubar mana da kima a wurin al’ummar Jihar Kano,” inji shi.

Har ila yau Jam’iyyar PDP ta zargi APC da lalata mata allunan tallar ’yan takararta a wurare da dama a jihar inda ta ce ba za ta ci gaba da zura ido ana yi mata cin kashi aka ba.

Kwamared Abdussalam ya yi kira ga hukumomin tsaro a jihar su dauki matakin da ya dace ba tare da nuna wariya a tsakanin jam’iyyu da ke jihar ba. “Muna sane da yadda ’yan sanda a jihar nan suka yi shiru game da abubuwan da suke faruwa ba tare da tsawatarwa ba. An kashe mutum akalla tara a tarurrukan APC amma har zuwa yanzu ba mu ji an kama masu laifin ba ballantana a gurfanar da su a gaban kotu. Sai dai duk da haka muna sa ran ’yan sanda su yi abin da ya dace wajen gudanar da aikinsu kamar yadda dokar kasa ta umarce su,” inji shi.

Jam’iyyar ta yi kira ga al’ummar jihar musamman magoya bayansu su ci gaba da zama masu bin doka da oda, tare da mayar da hankuli wajen ganin an yi nasara a zabe ba wai kula da zantuttukan harzukawa daga yayan Jam’iyyar APC ba.