Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

PDP za ta gurfanar da Hukumar Zaben Jihar Jigawa a gaban Kotu

PDP-logo

Jam’iyyar PDP reshen Jihar Jigawa za ta gurfanar da Hukumar Zabe ta  Jihar a gaban kotu saboda hana jam’iyyar shiga zaben kananan hukumomi da hukumar ta shirya za ta gudanar  a gobe Asabar  29 ga Yunin da mu ke ciki.

Shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Gabas Malam Aminu Jahun ya sanar da haka a wani taron manema labarai da ya kira, inda ya ce ba a yi musu uziri ba, ba a daga musu kafa ba kuma ba a ba su lokaci ba, an ba su lokaci kurarre dan haka za su je kotu domin su nemi ta hana gudanar da zaben, domin su samu damar shiga zaben.

ADVERTISEMENT

Ya yi korafin cewa a wancan zaben da aka yi, haka aka yi amfani da wadansu mutane wadanda ba ’ya’yan jam’iyyarsu ba ne aka hana su shiga zabe bayan sun biya kudin ’yan takararsu har Naira miliyan  64, kuma ba a mayar musu da kudin ba. Ya ce za su nemi kotun ta sa hukumar zaben ta biya su Naira miliyan 600 saboda an jima ana juya kudin nasu

Aminu Jahun ya ce sun yi duk abin da ya kamata don ganin sun shiga zaben an fafata da su amma an hana su shiga zaben saboda ba a sanar da su ba a kan lokaci. Ya kara da cewa ba a bar su, su shiga zaben kananan hukumomin ba, wanda abu ne da ya zama dole a bar su a matsayinsu na ’yan kasa masu ’yanci kamar kowa. Saboda dokar kasa ta ba su da ma, don haka babu wanda ya isa ya danne musu damarsu

ADVERTISEMENT

Kakakin Hukumar Zabe ta Jihar da ya yi magana da ’yan jarida a madadin Kwamashinan Hukumar Zabe ta Jihar, Habibu Yarima ya ce ba maganar wani kudi da Jam’iyyar PDP take bin hukumar kuma babu wata magana ta hana su shiga zaben. “Su ne dai ba su shiga ba, kuma ko da su ko babu su za mu gudanar da zaben saboda babu wata ka’ida da hukumar ta saba,” inji shi.