✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP za ta kwace mulki daga hannun APC a Yobe – Karasuwa

Shugaban Jam’iyyar PDP reshen Jihar Yobe Alhaji Gana Karasuwa ya ce jam’iyyar ta shirya tsaf don kwace mulkin jihar daga hannun Jam’iyyar APC da ta…

Shugaban Jam’iyyar PDP reshen Jihar Yobe Alhaji Gana Karasuwa ya ce jam’iyyar ta shirya tsaf don kwace mulkin jihar daga hannun Jam’iyyar APC da ta shafe sama da shekara 15 tana mulkin jihar ba tare da al’umma sun gani a kasa ba.
Alhaji Gana Karasuwa ya bayyana haka ne tattaunawarsu da Aminiya a Damaturu, inda ya ce yanzu haka kan ’ya’yan Jam’iyyar PDP a hade yake kuma sun gama shiri tunkarar zabe mai zuwa don kawo gwamnatin da za ta dama da kowa, maimakon gwamnatin da ya kira ta kama- karya da ta zama ta ’yan uwa da abokai.
Ya ce al’amarin siyasa wani abu ne na tuntuba da sanin madafa, kuma suna aiki tukuru domin ganin sun kara hada kan ’ya’yan PDP a jihar da dinki duk wata baraka a tsakaninsu ta yadda za su samu nasara a zaben da ke tafe.
Alhaji Karasuwa ya ce gwamnatin jihar da aka jarrabi jama’a da ita babu abin da ta kulla musu, a kullum jama’a fama suke yi da wahala, kuma saboda haka ne jama’a suka dawo daga rakiyarta suka hada kansu don sauya ta da gwamnati mai adalci.
Shugaban PDP ya nanata cewa, “Mun tabbata al’ummar Jihar Yobe sun san ciwon kansu kuma sun gane ma’anar siyasa tare da kwatanta jihar da sa’o’inta, inda za su gano cewa an yi wa tasu fintinkau; kullum jama’a sai dada fahimtarmu suke yi da kuma kokarinmu na jawo hankalin Gwamnatin Tarayya don ta gudanar da muhimman ayyuka a jihar.”