✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Petr Cech zai yi ritaya daga kwallon kafa

Golan Kungiyar Arsenal ta Ingila, Peter Cech ya sanar da cewa zai rataye takalman kwallonsa bayan kakar wasannin bana. Peter Cech dai ya yi kimanin…

Golan Kungiyar Arsenal ta Ingila, Peter Cech ya sanar da cewa zai rataye takalman kwallonsa bayan kakar wasannin bana.

Peter Cech dai ya yi kimanin shekara 20 yana tsaron gida, inda ya yi shekara 15 a gasar Firimiyar Ingila kawai.

Ya zo Kungiyar Chelsea ne daga Kungiyar Rennes ta Faransa a shekarar 2004, sannan bayan shekara 11 ya koma Arsenal a shekarar 2015.

A tsawon zamansa a Ingila, Peter Cech ya lashe duk kofunan da dan wasan kwallon kafa yake bukatar lashewa kamar su gasar Zakarun Turai da Firimiya da kofin Kalubale da sauransu.