Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Pillars ta lashe Kofin Ahlan

Kungiyar  Kwallon kafa ta Kano  Pilars ta zama zakara a gasar cin Kofin Ahlan inda ta doke takwararta ta Wikki Tourist ta Bauchi da ci 2-1 a wasan karshe da aka fafata a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

Gasar ta cin Kofin Ahlan Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Jihar Kano Alhaji Dokta Sharif  Rabi’u Ahlan ne ya dauki nauyinta wadda kuma ake gudanarwa duk shekara a tsakanin kungiyoyin wasannin kwallon kafa da ke kasar nan.

ADVERTISEMENT

Kungiyar Wikki ce ta fara jefa kwallo a ragar Pillars kafin Auwalu Ali wanda aka fi sani da Malam na kungiyar Kano Pillars ne ya farke kwallon kafin Adamu Hassan ya ci kwallo ta biyu da ya ba kungiyar ta Pillars nasarar lashe wasan bayan da aka dauki kimanin minti 35 ana gudanarwa.

Bayan an kammala gasar an fitar da wadanda suka nuna hazaka a wasan inda aka ba Auwalu Ali dan wasan Pillars kyautar dan wasan da ya fi kowa yawan zura kwallaye a raga. Haka kuma an ba mai tsaron gidan Pillars Danladi Isah kyautar Golan da ya fi kwazo.  Har ila yau Kabiru Baleriya ya samu kyautar kocin da ya fi kowane koci ba ’yan wasa horo. Sai kuma Kungiyar  Yobe Desert Stars ta zama gwarzuwar kungiyar wasan kwallon kafa a gasar.

ADVERTISEMENT

A jawabinsa na rufe gasar Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dokta Nasiru Yusuf Gawuna ya jinjina wa wanda ya dauki nauyin shirya gasar Dokta Sharif Rabi’u Inuwa Ahlan inda ya yi alkawarin samun goyon bayan gwamnatin jihar a duk wani abu da zai bunkasa harkar wasanni a jihar.

Dokta Gawuna ya taya wadanda suka samu nasara murna tare da kira gare su da su zage dantse don fuskantar gasar da ke gabansu ta rukuni-rukuni ta kasa ta shekarar 2018 zuwa 2019.