Da Dumi Dumi

Pogba ya kaddamar da asusun tallafa wa masu  cutar Kurona

Paul Pogba

A ranar Lahadin da ta gabata ce dan kwallon kulob din Manchester United da ke Ingila haifaffen Faransa, Paul Pogba ya kaddamar da asusun tallafa wa wadanda suka kamu da cutar Kurona.

Pogba ya sanar da haka ne  a shafin sadarwarsa na Facebook a ranar da ya yi bikin cika shekara 27 da haihuwa, inda ya nemi takwarorinsa da su ma su kaddamar da irin wannan asusu don a taimaka a yaki cutar Kurona da yanzu ta addabi duniya.

Dan kwallon ya ce yana sa ran zai tara akalla Fam dubu 27 a rana daya (kimanin Naira miliyan 12 da dubu 700).

Ya ce ya yi haka ne don ya bayar da tasa gudunmawa wajen yakar cutar da kuma taimaka wa gajiyayyu musamman yara wadanda suka kamu da cutar.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya