✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Raba siyasa da addini

Lokuta da yawa wasu mutane suna magana akan cewa siyasa daban addini daban wanda kuskure ne. Domin wannan ya sabawa falsafar musulunci da kuma tarihin…

Lokuta da yawa wasu mutane suna magana akan cewa siyasa daban addini daban wanda kuskure ne. Domin wannan ya sabawa falsafar musulunci da kuma tarihin musulunci. Saboda Allah (S.W.T) shi ne ya halicce duniya da halittun dake cikin ta wadanda suka kunshi; duwatsu, gulabe, shukoki, mutane, halittu kanana da kuma manya, har da abubuwa wadanda ido baya iya riskarsu, hannu baya iya tabawa, hanci baya iya jin kamshinsu, harshe baya iya jin dandanon su.

Sannan bayan kasancewar duniya da abin da ke cikin ta mallakarSa; Allah (S.W.T) shi ne masanin komai (abunda ya faru, da wanda ake akai yanzu, dama wanda zai faru a gaba). Saboda wannan dalilin; Allah (S.W.T) shi ne ya cancanta ya tsara dokokin da za a bi gurin zama a cikin duniya. Wasu dalilai dake sa mutane wannan tunanin shi ne, fakewa da addini da wasu tsiraru ke yi suna yaudarar mutane a siyasa.

Ma’anar addini A gurin Turawa

Wani zai yi tambayar cewa “Me ya sa mutane suke yin wannan tunanin na cewa siyasa daban addini daban?” Amsa ita ce tunanin Yammacin duniya (Turawa) ne yake tasiri a kansu. Har ya sa suka zama masu bin mazhabar ‘Secularism’ (tsame addini daga shugabanci da harkokin yau da kullum) ba tare da sun farga ba. Kuma asalin wannan fahimtar za ta iya zama haihuwar masu wannan fahimtar da aka yi a cikin ballagazar kasa ‘secular state.’ Saboda addinin da Turawa suke kai a ‘Zamanin Tsakiya’ (middle ages-shekarun da Nahiyar Turai take cikin duhun jahilci da kauyanci) da kuma bayan yin abin da ake kira ‘Renaissance’ shi ne; addinin Kiristanci. Shi kuwa addinin Kiristanci ba ya da wani tsari na shugabanci wanda za a ce ya samo asali daga Annabi Isa (AS).

Saboda Annabi Isa (AS) tsawon da’awarsa shekara uku ce, inda a cikin shekara ukun bai samu damar kafa cikakken gari don mulkar al’ummar da suka yi imani da shi ba. Wanda shi ne zai sa tsarin da ya mulki al’umma a lokacinsa ya zama abin koyi ga sauran shugabannin Kiristocin da za su biyo baya ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa malaman coci-coci da sarakunan gargajiya suka rika tafiyar da shugabanci bisa son ransu inda ya kai ga gazawar tsarin tattalin arziki na ‘babakere’ (feudalism) a  shekarun tsakiyar zamani.

Bayan gazawar malaman coci-coci da sarakuna da tsarin tattalin arziki na ‘babakere’  wadda ta zama Jari-Hujja wurin warware matsalolin Turawa. Masu akidar ‘Ballagazanci’ daga cikin Turawa suka ga ya dace a ɗabbaƙa akidar a aikace ta hanyar raba addini da siyasa da sauran al’amurran yau da kullum, inda suka takaita ma’anar addini da cewa addini shi ne: “alaka a tsakanin mutum da Mahalicci,”  shi kuma coci ma’anarsa ita ce “Hukumar da ke da karfin fassara Baibul da kuma saka dokokin da za a bi wurin bauta wa Mahalicci.”

Daga nan akidar Ballagazanci ‘secularism’ ta ci gaba da samun gurbin zama a zukatan Turawa har zuwa yau. Bugu da kari, akidar ballagazanci (raba addini da rayuwa) ta taimaka sosai wurin dawo da tsofaffin akidu da kuma haihuwar sababbi wadanda suke karfafa wa mutane bauta wa tunaninsu, ta hanyar bin abin da zuciyarsu ta raya musu a harkokin yau da kullum kamar “democracy” dimokuradiyya da “Atheism” bautar gumaka, da “Agnosticism” bautar son rai, da “Secular-capitalism”, ballagazanci na Jari-Hujja da bin akidun su Darwin da gurguzu da kwaminis da tsaka-tsaki da fifita abin duniya a kan dan Adam da harkokin da suka jibanci ’yancin jinsi irin su (Socialism, Communism, Fascism, Nazism, Liberalism, Materialism, Feminism) da sauransu. Dukkan wadannan akidu sun samo asali ne sakamakon cire addini da mutane suka yi a cikin lamuransu na yau da kullum suka koma bauta wa tunaninsu. Akidar kuma ta taimaka wurin tsame addini a harkokin ilimi aka koma ballagazzajen ilimin kimiyya (secularization of sciences).

A wasu lokuta za a ji wadansu Kiristoci suna na’am da wannan tsarin na cire addini daga cikin harkar shugabanci ko siyasa ko ilimi ko kiwon lafiya ko tattalin arziki. Ta hanyar cewa a cikin Matta: 22:21. Annabi Isa (AS) ya ce “Render unto Caesar the things that are Caesar’s, and unto God the things that are God’s.” Suna fassara wannan aya da cewa: Annabi Isa (AS)  ya ce “A bar wa Kaisar (Shugaban Rumawa) mulkin al’amurran yau da kullum, shi kuwa Allah a bar maSa gefen bauta.” Don haka a tunaninsu raba addini da siyasa ya samo asali ne tun zamanin Annabi Isa (AS). Wanda da waccan ayar da kuma bata waccan fassarar hadi da tasirin rubuce-rubucen Paul (wani malamin Kirista) da ke a Sabon Alkawari ‘New Testament’ suna daga cikin hujjojin Kiristoci na rashin bin tsarin addini a cikin harkokinsu na yau da kullum, (suka rika ganin addini kawai a coci ake yinsa ranar Lahadi kuma a can ake barinsa).

A addinin Kirista cin riba, zina, caca, naman alade, shan giya, shigar batsa duk haramun ne, amma Kiristoci suna aikata wadannan abubuwa. Wannan ya sa wadansu malaman Nazarin Addinai ‘Comparatibe Religion’ suke kiran Kiristanci da Western Cibilization (Wayewar Turai). Shi ya sa abu ne mai wuya a ga littafin addinin Kirista da ke magana a kan shugabanci ko tattalin arziki da sauran fannonin mu’amala.

A karshe masu wannan akida ta raba addini da siyasa ya kamata su san cewa addinin Musulunci ba kamar Kiristanci ba ne. Domin Kur’ani da hadisai sun yi magana a kan shugabanci. Sannan Annabi (SAW) ya kafa al’umma wacce ya shugabanta tsawon shekara 23 ta hanyar yi musu hukunci da abin da aka saukar a gare shi (Kur’ani). Sannan wadanda suka zo bayansa sun yi shugabanci bisa Kur’ani da Hadisi, kamar Abubakar (RA), Umar (RA), Usman (RA), Aliyu (RA) da sauransu. Don haka maganar cewa a cire siyasa a addini kuskure ce babba. Kuma malaman Musulunci da yawa sun yi rubutu a kan shugabanci/siyasa da tattalin arziki a mahangar Musulunci. Ko a nan Arewa an samu shugabanci kan tafarkin addinin Musulunci a lokacin Sheikh Usman Dan Fodiyo da sauran shugabannin da suka zo bayansa kafin zuwan Turawa.

Allah Ya shirya mu, Ya sa mu fi karfin zuciyarmu kuma Ya ba mu ikon bin daidai a koyaushe.

Yana da kyau mutane su gane wannan, kuma su fahimci siyasa da kuma addini. Allah Ya yi mana jagoranci.

Yakuba Usman da Nura Mai Apple, su aiko wannan rubutu ne daga Gusau Jihar Zamfara. kuma za a iya samunsu ta: 08166756463 da  08133376020.