✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rafi ya hallaka budurwa kwana biyar kafin aurenta

A ranar Lahadin da ta gabata ce wata budurwa mai suna Farida Saminu ta rasa ranta sakamakon nutsewa cikin ruwa da ta yi a lokacin…

A ranar Lahadin da ta gabata ce wata budurwa mai suna Farida Saminu ta rasa ranta sakamakon nutsewa cikin ruwa da ta yi a lokacin da matukin Keke NAPEP din da take ciki ya yi kokarin tsallake gadar Hayin Malam Bello da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Budurwar ta rasu ne kwana biyar kafin aurenta kuma tana hanyarta ce ta zuwa gyaran jiki da amare ki yi, kuma har zuwa lokacin hada wannan labari ba a ga gawarta ba.

Lamarin ya auku ne da misalin karfe 6:00 na yamma lokacin da ruwan rafin ya hau kan gadar unguwar sakamakon ruwan sama mai karfi da aka yi.

Wadansu daga cikin wadanda lamarin ya auku a gabansu sun cewa jama’a da yawa ne suka tsaya a bakin titi ganin ruwan ya haura kan gadar amma sai matukin Keke NAPEP din ya yi kokarin wucewa ta cikin ruwan wanda hakan ya sa ya kife da su.

A cewar wani mai shago a kusa da wurin da abin ya faru wadansu matasa sun shiga cikin ruwan  inda suka ceto wadansu daga cikin mutanen da ke cikin Keken, amma ita amaryar ruwa ya tafi da ita.

Kakan marigayiyar Alhaji Husaini Garba, ya shaida wa  Aminiya cewa abin ya dame su amma hakuri ya zama dole.

“Ni ne mahaifin mahaifiyarta kuma a wajena ta girma har na saka ta makarantar zuwa Kwalejin Koyon Aikin Asibiti. Kuma ’yan kwanaki suka rage ta yi aure lamarin ya faru. Gaskiyar abin da ya faru shi ne ba rabon katin aure ta je ba, ta tafi gyaran jiki ne da ake yi. Kuma wannan rana ta fada min cewa za ta rika zuwa gyaran jikin ne har kwana bakwai. Da za su tafi sai ta nemi wani yaro a gidan mai suna Kabiru ya raka su, su uku suka tafi sai aka dauki karin mutum biyu amma da suka shiga ruwan da nufin wucewa sai shi Kabiru kasancewarsa namiji sai ya koma gaban Keken ya zauna. Suna shiga ruwan da Keken ya fadi sai ya rike ta da karfi amma ruwan sai ya fisge ta.

Kuma mun samu labarin cewa akwai wani yaro da ya yi kokarin fito da ita daga cikin ruwan wanda shi ma har yanzu ba a gan shi ba. Mun je bakin kogin amma har yanzu babu labarinsu. Fatarmu dai Allah Ya jikansu da rahamarSa,” inji shi.

Wakilinmu ya zanta da wanda za ta aura mai suna Mubarak Ibrahim, inda ya ce har yanzu bai yarda ta rasu ba, domin a ransa ji yake kamar za ta dawo tunda har yanzu ba a ga gawarta ba.

“Na dangana al’amarina ga Allah amma ni fa har yanzu ji nake kamar ba ta rasu ba domin har yanzu ban mika wuya ba. Ji nake kamar tana raye domin Juma’ar nan fa mai zuwa (yau) ne bikinmu sai wannan abin ya faru. Idan har ka ga na mika wuya to sai na ga an kawo Farida cikin likkafani amma idan ban ga Farida ba ko shekara nawa ne ba zan yarda ta rasu ba.

“Sai na ga gawar Farida,  hankalina zai kwanta. Yanzu tunanina shi ne wane hali take ciki domin a yanzu na kasa sukuni na kasa yin komai, babban burina a ce an ganta ko a raye ko a mace  kafin hankalina ya kwanta,” inji shi.

Haka akwai wani matashi mai suna Abdullahi da aka ce shi ma ya shiga ruwan da nufin ceto budurwar wanda shi ma ake tsammanin ya rasa ransa domin har lokacin hada wannan labarin ba a gan shi ba. An ce yana sana’ar gyaran babur ne a kusa da gadar na rafin unguwar Hayin Malam Bello.

Yayan matashin mai suna Umar ya ce tunda Abdullahi ya shiga rafin da nufin ceto Farida ba a gan shi ba.

“Da shi aka ceto wata mata daga cikin Keken shi ne sai ya sake komawa cikin ruwan domin ceto budurwar kuma tun daga lokacin ba a gan shi ba,” inji shi.

Aminiya ta fahimci cewa wannan gada ta Hayin Malam Bello duk shekara idan aka yi ruwan sama mai yawa yakan shanye ta na tsawon wasu mintuna wanda hakan ke hana mutane wucewa.