Search
Subscribe
Rage yawan Kanawa

Rage yawan Kanawa

A ranar Larabar makon jiya (8/5/2019) gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu a kan dokar kirkiro sabbin masarautu da majalisar dokokin jihar ta tura masa wanda ya sanya yanzu ake da masarautu guda biyar a jihar Kano maimakon guda daya da ta dade tana da ita.

Sabbin masarautun dai su ne: Kano mai kananan hukumomi goma, sai Rano ita ma kananan hukumomi goma, sai Gaya mai kananan hukumomi takwas da Karaye mai kananan hukumomi bakwai da kuma Bichi da ke da kananan hukumomi tara.

Kafin a kirkiro da sabbin masarautun, jihar Kano baki dayanta tana karkashin masarautar Kano ce, watau daukacin kananan hukumomi 44 na jihar Kano duk suna karkashin masarautar Kano ne, shi ya sanya duk wanda ya fito daga jihar Kano ake kiransa Bakano, domin shi dan kasar Kano ne.

Amma yanzu a sakamakon kirkiro da sabbin masarautu da Gwamna Ganduje ya yi, yanzu kanawa sun koma suna da kananan hukumomi 10 ne kawai, watau Kano Municipal da Nasarawa da Kumbotso da Ungogo da Dala da Tarauni da Fagge da Gwale da Dawakin Kudu da kuma Minjibir.

Wannan yana nufin a halin yanzu wadanda ba su fito daga wadannan kananan hukumonin ba sun zama ba kanawa ba ne, wadanda suka fito daga kananan hukumomi goman nan su ne kanawa a halin yanzu, domin a kasar Hausa ana danganta mutum ne da masaraurar da ya fito.

Saboda haka yanzu a jihar Kano za a iya cewa ana da Kanawa ke nan da Gayawa da Ranowa da Bichinawa da kuma Karayawa. A sakamakon wannan canjin da aka samu na fahimci cewa shi kansa mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje yanzu ba bakano ba ne, shi Babiche ne.

Tun da aka kirkiro jihar Jigawa aka fara rage wa kanawa yawa, domin kafin lokacin duk wanda ya fito daga jihar Kano a wancan lokacin ana yi masa kallon Bakano ne saboda lambar Kano da za a gani a motarsa ko kuma saboda jin cewa shi dan jihar Kano, kamar yadda a yanzu haka ake kallon mutumin da ya fito daga kasar Daura a jihar Katsina a matsayin Bakatsine.

Shi dai mai girma gwamna, ya ce ya amince da kara masarautu a jihar Kano ne domin a ganinsa za su taimaka wajen inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya da tsaro da sauransu.  Sai dai kuma abin da ke daure kai shi ne, ana nufin hakimai da dagatan da ke yankunan da aka kirkiro da masarautun sun kasa gudanar da wadannan ayyukan ne sai sarakunan yanka ne za su iya? Domin ni dai ban taba samun labarin wata masarauta da ta gina makaranta ko asibiti ba. Shi kansa Gwamna Ganduje ya tabbatar da cewa sarakuna suna karkashin kabanan hukumoni ne, to wanda yake karkashin shugaban karamar hukuma mai zai iya?

Tun zamanin turawan mulkin mallaka ake ta kokarin rage darajar sarakuna, sai dai kuma.shi bature saboda tsananin wayonsa lokacin da ya shigo kasar Hausa ya fahimci sarakuna suna da daraja da tasiri sosai don haka bai yi watsi da su gaba daya ba, sai ya yi amfani da su wajen gudanar da mulkinsa, amma ya dasa masu bishiyar da za ta taso ta cinye su.

Haka bature ya tafi ya bar ‘yan Najeriya suna ta ba wannan bishiyar ruwa tana kara girma, har aka zo shekarar 1975 lokacin da aka kafa wani kwamiti game da kananan hukumomi a karkashin shugabancin marigayi Sultan Ibrahim Dasuki, da aka kira shi ‘Kwamutin Dasuki,’ inda wannan kwamitin ya sa aka mayar da sarakuna karkashin kananan hukumomi.

Kafin wannan lokacin sarakuna suna karkashin (Natibe Authority) ne kuma sarakuna ne shugabanni, inda suke da iko da alkalai da ‘yan doka da gidajen kurkuku da sauransu, amma daga shekarar 1975 aka fige masu fikafukai, inda suka koma ma’ajiya al’adu kawai.

Shi ya sanya marigayi sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya bayyana matsayin sarakuna da cewa, “Da mu muke yi, aka zo ana yi da mu, yanzu sai dai a yi a fada mana.” A halin ma sai dai su ga ana yi,  ba a ko fada masu.

Da ma can a baya marigayi Malam Aminu Kano ya taba hasashen cewa lokaci zai zo da talaka zai daina jin tsaron sarki, har ma za ta kai ga talaka zai zo ya wuce ta gaban  sarki, sai dai ya ce masa ‘sannu sarki,’ saboda rashin tsoronsa da kuma ganin girmansa.

Saboda haka idan dai don cigaba ne aka kirkiro sabbin masarautu a jihar Kano, a gaskiya da sake. Domin babu wadansu ayyuka na cigaba da fadar sarki za ta iya samarwa, mutanen da aka nada a matsayin sarakuna ne kawai miyarsu za ta kara ja, domin za a yi amfani da kudin talakawa a gina masu fankacecen gida, a saya masu maka-makan motoci tare da makeken albashi da akawus-alawus da sauran abubuwa na alfarma.

Wannan ya sanya yanzu nauyi ya karu ga gwamnatin Kano, saboda maimakon dawainiya da sarki guda da take yi a baya yanzu sarakuna biyar za ta rika yi wa dawainiya da kudin da ya kamata a yi wa talakawa aikin samar da ruwa da wuta da ilimi da lafiya da tsaro da sauransu.

Yakamata ‘yan siyasa su rika yin la’akari da abubuwan da mutanensu za su amfana da su kai tsaye, maimakon mayar da hankali kan abubuwan da wadansu mutane ‘yan kalilan ne kawai za su amfana da su, domin cimma buri irin na siyasa.

Malamai dai suna cewa ‘gaggawa aikin shaidan ne,’ saboda haka sau da yawa aikin da aka yi shi cikin gaggawa ba ya karko.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin