✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rahama Sadau ta kammala jami’a a Cyprus

A wannan mako ne fitacciyar jarumar nan ta Kannywodd Rahama Sadau ta kammala karatunta na jami’a a kasar Cyprus. Jarumar ta karanci Harkokin Kula da Ma’aikata…

A wannan mako ne fitacciyar jarumar nan ta Kannywodd Rahama Sadau ta kammala karatunta na jami’a a kasar Cyprus.

Jarumar ta karanci Harkokin Kula da Ma’aikata ne (Human Resource Management), a Tsangayar Harkokin Kasuwanci da Tattaliln Arziki na Jami’ar Eastern Mediterranean da ke Kudancin kasar Cyprus.

Jarumar ce ta sanar da kammala karatunta tare da sanya hotunanta  da abokan karatunta a shafinta na Instagram.

Tuni jaruman Kannywood da sauran masoya suka rika taya ta murna da fatan alheri. Daga cikin wadanda suka taya jarumar murna, akwai Ali Nuhu wanda ya wallafa cewa, “Ba sauki irin yadda kika yi ta zirga-zirga tsakanin tafiya makaranta da kuma aiki. Amma ina alfahari da yadda kike dage kika kammala karatun nan. Ina alfahari da ke.” Sannan ta mayar masa amsa da cewa, “Cikin mutunci da girmamawa, ina matukar godiya.”

Sauran jaruman da suka taya ta murna akwai Maryam Yahaya da Maryam Gidado da Abdul M Sharif da Rabi’u Rikadawa da sauransu.