Da Dumi Dumi

Rahama Sadau ta taimakawa almajirai da kayan sanyi

Kasancewar lokacin sanyi ya shigo musamman a Arewacin Najeriya da abin ya fi kamari, Jaruma Rahama Sadau ta tallafawa almajirai da kayan sanyi a Unguwar Rimi Kaduna.

Jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram cewa, “mun zagaya jiya. Da dama daga cikin almajirai sun yi barci cikin natsuwa. Muna godiya ga wadanda suka bayar da gudunmuwa. Allah Ya saka. Yanzu muka fara,” inji ta.

Tun farkon makon nan ne jarumar ta wallafa a shafin nata cewa tana neman tallafin gawan sanyi domin tallafawa almajirai a karkashin Gidauniyar Ray Of Hope Foundation, inda ta ce, “bai kamata a yi watsi da almajirai ba. Iska daya muke shaka. Ya kamata mu hada hannu wajen taimakon almajiran nan fisabilillah. Mu taimaka musu da riguna a wannan lokacin. Ina bukatar mutum shida: Ali Jita da Hadiza Gabon da Adam A. Zango da Umar M. Shareef da Sadiq Sani Sadiq da su yi amfani da damarsu wajen isar da sakon nan kuma su taimaka. Kai ma za ka iya neman abokin na ya taimaka wajen bayar da gudunmuwa ko yada bukatar nan.”

Wasu daga cikin kayan sanyin da aka raba Hoto: Shafin Rahama na Instagram

 

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya