✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rahoto ya zargi tsohon Shugaban Gambiya da laifin fyade

Wata matashiya mai shekara 23 kuma tsohuwar sarauniyar kyau ta kasar Gambiya, Fatou “Toufah” Jallow, ta ce tsohon Shugaban Kasar Yahya Jammeh ya yi mata…

Wata matashiya mai shekara 23 kuma tsohuwar sarauniyar kyau ta kasar Gambiya, Fatou “Toufah” Jallow, ta ce tsohon Shugaban Kasar Yahya Jammeh ya yi mata fyade a lokacin da yake shugabanci.

Bayanan nata na kunshe ne cikin wani rahoto na Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Human Rights Watch da hadin gwiwar Trial International suka fitar inda aka yi bayanin zargin wani fyaden da Mista Jammeh ya yi.

BBC ta yi kokarin tuntubar Mista Jammeh, wanda a yanzu yake gudun hijira a kasar Ekuatorial Guinea, don jin ta bakinsa kan zarge-zargen.

Wani mai magana da yawun jam’iyyarsa ta APRC ya yi watsi da zarge-zargen da ake yi wa Mista Jammeh.

“A matsayinmu na jam’iyya kuma al’ummar Gambiya mun gaji da irin wadannan zarge-zarge da ake yi wa tsohon shugabanmu,” kamar yadda Ousman Rambo Jatta, ya fada a sakon da ya aike wa BBC.

“Tsohon shugaban ba shi da lokacin da zai mayar da martani kan wadannan karairayi. Shi mai mutunci ne kuma mai tsoron Allah wanda yake girmama matan Gambiya,” a cewar Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APRC.

Jallow ta shaida wa BBC cewa tana son haduwa da Jammeh, mai shekara 54, a kotu don ya fuskanci hukunci.

“Na yi matukar kokarin boye wannan labarin na kuma goge shi don ya kasance ba ya cikin tarihina.

“Amma a zahirin gaskiya na kasa yin hakan don haka na yanke shawarar yin magana a yanzu saboda lokaci ya yi da zan bayyana labarin na kuma tabbatar da cewa Yayha Jammeh ya ji abin da ya aikata.”

Ta ce tana kuma so ta bayar da shaida a gaban Kwamitin Fadar Gaskiya da Sasantawa na Gambiya, (TRRC), wanda Shugaba Adama Barrow ya kafa, bayan ya lashe zabe a watan Disambar 2016.

Shi dai  Yahaya Jammeh an tumbuke shi daga mulki ne a watan Janairun 2017 bayan da shugabannin yankin Afirka Ta Yamma suka tura dakaru lokacin da ya ki ya mika mulki.