✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rahoton Transparency kan rashawa a Najeriya ba daidai ba ne – Gwamnati

Gwamnatin Najeriya ta musanta rahoton kungiyar Transparency International (TI) wanda ya sanya ta a matsayin kasa mafi cin hanci da rashawa a yankin Afirka ta…

Gwamnatin Najeriya ta musanta rahoton kungiyar Transparency International (TI) wanda ya sanya ta a matsayin kasa mafi cin hanci da rashawa a yankin Afirka ta Yamma.

A wani rahoto da ta fitar na shekarar 2019 a jiya Alhamis, kungiyar mai sa ido kan cin hanci da rashawa ta ce Najeriya ta samu maki 26 cikin 100 a fannin kasashen da cin hanci da rashawa ya yi wa katutu, wanda ragin maki daya ne daga 27 da ta samu a 2018.

Rahoton na 2019 wanda ya bincika kasashe 180, ya saka Najeriya a mataki iri daya da kasashen Iran da Honduras da Guatemala da Bangladesh da Mozambique da kuma Angola. Sannan ya ce, sayen kuri’u a lokutan zabe ne ya kara jefa Najeriya cikin kangin rashawa.

Yayin da yake mayar da martani kan rahoton, Ministan Shari’ar Najeriya Abubakar Malami, ya ce akwai karancin hujjoji da za su tabbatar da sahihancin sakamakon binciken, wanda ya ce Najeriya ce ta 146 cikin kasashe 180 a shekarar 2019.

Malami ya yi martanin ne yayin da ya bayyana a shirin LunchTime Politics na kafar talabijin ta Channels, inda ya ce “Indai a bangaren yaki da cin hanci ne to mun yi kokari.”

Ya ci gaba da cewa: “Mun yi kokari sosai sannan kuma za mu ci gaba da yi. Duba da yadda muke da zimmar kawo karshen cin hanci ba sai na yi magana kan rahoton Amnesty ba.

Da yake nasa martanin, Auwal Musa Rafsanjani wanda shi ne shugaban Transparency a Najeriya kuma shugaban kungiyar CISLAC, ya bayyana ta’ajibinsa game da yadda kasar ke ci gaba da fadawa cikin rashawa duk da shirye-shiryen da Shugaba Buhari ya bullo da su kamar Whistleblower wato shirin nan na kwarmata bayanai.