Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Raina Masarauta: Sarkin Rano na tuhumar Hakimai 4

Masarautar Rano a jihar Kano tana tuhumar Hakimai 4 saboda rainar masarautar, Hakiman da ake tuhuma sun hada da: Hakimin Karamar Hukumar Doguwa Alhaji Aliyu Harazimi da Hakimin Kura Alhaji Bello Ado Bayero da Hakimin Garun Malam, Alhaji Abubakar Gwadabe Buhari da kuma Hakimin Karamar Hukumar Takai Alhaji Lamido Danburan Haruna.

An aika wa Hakiman wasikar tuhumar ne a jiya Litinin 17 ga Yuni wanda Sakataren masarautar Rano Muhammad Idris Rano, ya rattabawa hannu, wasikar tana dauke ne da sakon gayyata a watan da ya gabata inda aka umarce su da su kai gaisuwa barka da shan ruwa na watan azumin Ramadan sannan su ziyarci fadar Sarkin don gudanar da hawam Sallah karama.

ADVERTISEMENT

Takardar ta umarci Hakiman da su amsa gayyatar masauratar a cikin awa 24 ko kuma a dau matakin ladabtarwa akan su.

ADVERTISEMENT