Da Dumi Dumi

Rainin wayo ne dora wa Fulani makiyaya hare-haren yankin Ibo

Hakika yadda ake jingina wa Fulani makiyaya alhakin hare-haren da ake kaiwa a wasu sassa na kasar nan musamman sashin Kudu, akwai aya tambaya a kai. Na san wane ne Bafulatani saboda ni Shuwa-Arab ne a daji aka haife ni kamar Bafulatani, tare muka taso da Fulani na san wane ne Bafulatani.  Mu da Fulani ba mutane ne masu son tashin hankali ba, muna fama da dabbobinmu, mu da rakuma Fulani da shanu, to me zai kai a ce wai mu ne muke daukar bindigogi kirar AK 47 muna kai hari a kan jama’a?  
Ya kamata manyanmu na Arewa su tashi su yi magana su daina yin shiru ana kokarin bata sunan jama’arsu bayan an san wadanda suke yin aika-aikar nan. A jiharmu ta Borno an taba kama mutanen yankin Neja-Delta dauke da makamai suna yin ta’asa a yankin Kala Balge a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan, an kama su suna kashe mana mutane. An kama ’yar Neja-Delta mace a garinmu Damboa tana kashe mana mutanenmu. Yanzu makiya Najeriya sun ga gwamnatin Buhari da gaske take yi wajen murkushe Boko Haram, sai suka bullo da batun wai Fulani makiyaya suna kai hare-hare a yankunansu da wasu yankuna da koda wasa ba zai yiwu Bafulatani ya dauki makami ya kai hari a wurin ba. Fulani nawa ne a yankin Kudu maso Gabas na ’yan kabilar Ibo da Kudu maso Kudu na kabilun Neja-Delta da za a ce wai suna kai farmaki a kauyuka har suna kashe mutane? Tun zamanin Shugaba Jonathan tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon ya fito ya shaida wa duniya cewa masu kai hare-haren nan ba Fulani ba ne, wadansu ’yan ta’adda ne da suka samu horo irin na soja suke yi wannan danyen aiki. An zo ana ta kashe mutane a yankin Agatu da ke iyakar jihohin Benuwai da Nasarawa ana ta dora wa Fulani, me zai hada Fulani fada da Agatu? Dukkanmu ’yan Arewa ne da ake nema lallai sai an hada mu fada da juna domin a cimma wata muguwar manufa ta wargaza mu.
To yanzu an dawo da zance cewa wai Fulani ne suke kashe Ibo da mutanen Neja-Delta a yankinsu. Kuma abin takaici har a samu wadansu mutane daga Arewa su rika yarda da wannan da ko tatsuniya iyakarta ke nan! Kwanaki an kashe mana mutane a Enugu an sanya su a rami a binne haka kawai, sannan a makon jiya a Abiya rigima ta tashi a tsakanin wani soja da wani dan kabilar Ibo, amma sai aka kama kashe mana mutanenmu na Arewa da ke can.
Na yaba yadda mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekwerimadu ya fito ya nemi a yi taka-tsantsan wajen dora wa Fulani makiyaya laifin hare-haren da ake kaiwa.
Kowa ya san Arewa ta zamo wurin da ’yan kabilar Ibo da dama suka taso suka zama fitattun mutane a kasar nan, amma abin mamaki wadansu da ba su san abin da suke yi ba, suna ta kokarin sai sun cutar da Arewa sun bata masa suna sun cutar da al’ummarta masoya zaman lafiya. Galibin masu wannan hali ba za su iya komawa jihohinsu na asali su iya zama ba, Arewa ta yi musu komai amma suna bin ta da sharri.
Don haka ya kamata masu hankali a cikin mutanen Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu su rika jan kunnen mutanensu.
Su tuna su ma fa akwai mutanensu jibge a nan Arewa, idan suka ci gaba da takalar mutanenmu musamman Fulani makiyaya da suke fada da dabbobinsu a daji, kada su sa ran mutanen Arewa za su kame hannuwansu su zuba musu ido.
Akwai rainin wayo sosai a rika dangana ayyukan ’yan ta’addan da suke Kudu a kan Fulani makiyaya, yaushe Bafulatni zai baro shanunsa a daji ya shiga gari ya kama fada da masu masaukinsa? Hare-haren da suke aukuwa a Kudu mutanensu marasa aikin yi da masu neman tara dukiya a bagas suke yin abinsu, amma sai a dora wa Fulani makiyaya saboda ba su da gata.
Shin ta ina wadannan Fulani suke iya ratsa tsakanin kauyukan Ibo su kai hari su koma daji ba tare da an kama su ba, sai dai a rika shiga kafafen watsa labarai ana ta zuba karya cewa Fulani ne, Fulani ne? Harin da aka kai Jihar Enugu kowa ya ji yadda Kwamishinan ’Yan sandan Jihar ya shaida wa duniya cewa harin bai da nasaba da Fulani makiyaya, fada ne a tsakanin kabilun Ibo su ya su. Amma domin a samu damar kashe wannan bayani nasa sai aka maza aka canja masa wurin aiki.
Don haka, kalubalen ne a kan shugabannin jihohin Arewa musamman gwamnoni da sarakuna su fito su yi magana da kakkausar murya kan wannan cin zarafi da ake yi wa jama’arsu. Ba dole ne a tilasta mana zama tare ba, duk wanda yake jin ya shirya wa ballewa daga Najeriya ya je ya yi ta ballewarsa, amma ya daina takalar wadanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba yana kashe na kashewa yana lalata dukiyar wanda ya ga dama tare da aikata ta’asa yana dora laifin hakan a kan wasu.  
Su kuma ’yan uwanmu Fulani a can Kudu da nan Arewa ya kamata su koma cikin hayyacinsu, su tsaya su gyara tsakaninsu, su kyautata dangantarsu da Allah, duk wani mai mugun hali a cikinsu ya daina, idan ba haka ba, wannan guguwa tana iya yi musu illa, domin Allah bai taimakon azzalumi a kan azzalumi, sai dai wanda ya fi karfin wani ya murkushe shi. Don haka wadanda ake hada baki da su suna cutar da Fulani ’yan uwansu da sunan satar shanu ko satar mutane ko duk wata barna su hanzarta tuba su koma ga Allah domin kare martabarsu da ta al’umarsu.
Alhaji Adam Shuwa Damboa,
Mpape, Bwari Area Council, Abuja  08055945695, 08034495570 

Share