✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rajistar Jam’iyyar APC: ‘An bude sabon shafin dimokuradiyya’

Shekaranjiya Laraba jam’iyyar All Progressibes Congress (APC) ta bayyana cewa yanzu an bude wani sabon shafin gudanar dimokuradiyya tunda yake Hukumar Zabe ta kasa (INEC)…

Tutar sabuwar jam’iyyar APC da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi wa rajista shekaranjiyaShekaranjiya Laraba jam’iyyar All Progressibes Congress (APC) ta bayyana cewa yanzu an bude wani sabon shafin gudanar dimokuradiyya tunda yake Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta tabbatar mata da matsayin da ta bukata na kasancewarta dunkulalla, bayan da jam’iyyu hudu suka narke cikinta.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar ta APC na rikon kwarya, Alhaji Lai Mohammed, a wani bayani da ya yi, ya taya ’yan Najeriya murna kan samuwar wannan muhimmin al’amari na tabbatuwar jam’iyyar ta APC.
Ya ce yanzu jama’ar Najeriya suna da wata kyakkyawar makoma da madogara daga jam’iyyar da ta dinga yi musu wuju-wuju ina Gabas take har na tsawon shekaru goma sha hudu.  “Kasancewar hukumar zabe ta kasa (INEC) ta amince da narkewar jam’iyyun siyasa cikin jam’iyya daya ta APC, yanzu an bude wani sabon shafin siyasa ga kasarmu da jama’arta da suka dade cikin magagi.  Muna godiya da’yan Najeriya na cikin gida da ketare da suka kasance tare da mu, suna ba mu karfin guiwa, a cikin wannan tafiya.  Muna godiya ga kafafen yada labarai saboda adalcin da suka yi mana da kuma ita kanta hukumar zabe da ta yi abin da ya kamata, ta kauda kai daga kwakyariyar wadansu kungiyoyin siyasa, don ta ki bin doka”. Inji shi.
Ya ce bayyanar jam’iyyar APC wata nasara ce ga Najeriya da kuma dimokuradiyya domin ta daukaka matsayinsu zuwa shiga tsara da kasashen da suka yi nisa a wannan fage na takarar fitattun jam’iyyu biyu.
“Tafiya ce mai nisa, wadda aka sha gumurzu a cikinta.  Ba irin yarfen da ba mu sha ba.  Mun tsallake turaku da tuddai masu yawa da tsuga-tsugai da aka kakkafa mana a wannan tafiya, amma saboda jajirjewarmu, ga shi mun kai gaci.  Duk mun yi wannan hobbasa ne kuwa saboda mu samar wa Najeriya matsayi ta zama kwangiri a tsakanin kasashen duniya da ake martabawa da girmamawa”.  Inji shi.
Ya ce, “Mun dauki alkawarin ba za mu ba’yan Najeriya kunya ba, musamman da yake mun hada wannan karfi da karfe ba don kawai mu yi shugabanci mu more ba, sai dai don mu maido da martabar kowane dan kasa don ya samu sakata da walawa”.
Wannan bayani na sakataren yada labaran ya biyo bayan sanarwar da sakataren hukumar ta INEC, Abdullahi A. Kaigama ya yi ne a shekaranjiya din cewa hukumar ta amince da tabbatar da narkewar jam’iyyun ACN da CPC da ANPP cikin sabuwar jam’iyyar APC, saboda haka an yi mata rajista.
Ya ce, “Bayan an duba takardar bukatar rajista, hukumar ta ga cewa jam’iyyun da ke son narkewa cikin jam’iyya daya ta APC sun cika dukan ka’idojin da ake bukata, saboda haka ta tabbatar da musu da wannan bukata.
“Da wannan amincewa hukumar ta tabbatar da janye dukan takardun shaidar jam’iyyun kuma za ta bayar da takardar shaidar jam’iyya guda ta APC”. Inji shi.