✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rakumi ya kashe matashi a Kebbi

Wani rakumi ya kashe matashi dan shekara 18 a Unguwar Koko, a Jihar Kebbi. Shaidu sun ce rakumin ya murkushe matashin ne, ya cije shi…

Wani rakumi ya kashe matashi dan shekara 18 a Unguwar Koko, a Jihar Kebbi. Shaidu sun ce rakumin ya murkushe matashin ne, ya cije shi sannan kuma ya ci gaba da zama a kansa har sai da ya mutu.

Marigayin wanda aka bayyana sunansa da Yunusa, ya hadu da wannan  tsautsayi ne, lokacin da ya dawo daga gona sai ya yi gamo da rakumin. Wani mai suna Muhammadu Garba ya ce, marigayin yana kan hanyarsa ta dawowa daga gona ce a kan keke, inda ya je domin girbin gero. Ya ce yadda abin ya faru shi ne, Yunusa ya fada wa rakumin ne da kekensa, inda shi kuma rakumin ya danne shi.

“Yana fadawa kan rakumin, sai ya fado kasa daga kan keken. Shi kuwa rakumin sai ya take shi da kafarsa, ya cije shi da bakinsa, daga bisani kuma ya murkushe shi. Mutane da ke wurin sun yi ta dukan rakumin da bulala da nufin ceto mamacin amma ya ki sakin matashin har sai da ya mutu. Kuma har lokacin da ya mutu, rakumin bai tashi daga kansa ba,” inji Muhammad Garba.

Shi ma wani shaid, Aliyu Koko ya ce tsoro ne ya hana shi zuwa kusa da rakumin, a lokacin da yake taka mamacin.

Kakakin ’Yan sandan Jihar Kebbi, DSP Danjuma Possi ya ce zuwa lokacin da wakilinmu ya tuntube shi, hukumar ’yan sandan ba ta samu rahoton faruwar lamarin ba.