✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan 1444: Yadda za a yi Sallar Tarawih a Massallacin Harami

Sheikh Shuraim ya yi bankwana da limanci a Masallacin Harami a yayin da ake shirin fara azumin Watan Ramadan

Hukumar Gudanarwar Masallatan Harami da ke Saudiyya ta tabbatar da ritayar Sheikh Sa’ud Ibrahim Shuraim, daga yin limanci a Masallacin Harami da ke Makkah.

Hukumar ta kuma sanar da haka ne kafin wayewar garin Alhamis, a sanarwar da ke dauke jerin jadawali da jerin sunayen limaman da za su jagoranci sallolin Tarawih da Tahajjud a masallatan Harami a watan Ramadan na shekarar 1444 Hijiriyya da zai kama a mako mai zuwa.

Sanawar ta bayyana cewa bayan amincewar Masarautar Saudiyya da ritayar Sheikh Sa’ud Shuraim ba zai jagoranci sallolin Tarawih da Tahajjud ba a bana, a Masallacin Haramin Makkah da ya saba limanci.

Wadanda za su yi limancin sallolin su ne:

1. Sheikh Abdul Rahman Sudais
2. Sheikh Bandar Baleelah
3. Sheikh Maher Al Muaiqly
4. Sheikh Yasir Ad Dawsary
5. Sheikh Abdullah Juhany

Sheikh Shuraim ya yi ritaya daga matsayinsa na daya daga manyan limaman masallacin ne bayan shekara 32 yana gabatar da hudubobi da jagorantar Sallar Juma’a da sauran salloli.

A ranar 6 ga watan Oktoba, 1991 ne aka nada Sheikh Shuraim limamin Masallacin Harami saboda dalilai na kashin kansa.

A baya Aminiya ta kaho rahoton cewa Sheikh Shuraim ya ki sabunta kwantaraginsa na limanci a masallacin, sai dai Hukumar Gudanarwar Masallatan Harami ko Masarautar Saudiyya ba su fitar da bayani a hukumace a kan hakan ba.

Sanarwa da Hukumar Masallatan Haramin ya fitar a ya kuma nuna jerin sunayen malaman da za su jagoranci sallolin Tarawih da Tahajjud a Masallacin Manzon Allah da ke Madina:

  1. Sheikh Ahmad Al-Huzaifi
  2. Sheikh Salah Budair
  3. Sheikh Abdulmuhsin Al-Kasim.

Takaitaccen tarihin Sheikh Shuraim

Alkaluman tarihi sun nuna an haifi Sheikh Sa’ud Ibn Ibrahim Ibn Muhammad Al-Shuraim a ranar 19 Janairu 1964 a birnin Riyadh na Saudiyya.

  • Sheikh Shuraim Farfesa ne a Fannin Shari’a da Darussan Musulunci a Jami’ar Umm Al-Kura da ke garin Makkah.
  • Baya ga kasancewarsa gangaran a haddar Al-Kur’ani, Sheikh Shuraim mai aikin yada da’awar Musulunci ne
  • Ya kammala digirinsa na farko a Jami’ar Umm Al-Kura a 1995
  • Shiekh Shuraim ya yi karatun firamare a Areen Elementary School.
  • Sannan ya yi karatun sakandare a Modern School for Secondary Education.
  • Sannan ya yi karatun gaba da sikandare a makaranatar Al-Yarmouk North High School wacce ya kammala a shekarar 1983.
  • Ya kuma halarci jami’ar Imam Muhammad Bin Saud, indq ya kammala a shekarar 1988.
  • Ya ci gaba da karatu har ya kai ga matakin samun shaidar digirin PhD.