Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta rage lokutan ma’aikata

Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da rage lokutan ma’aikatan jihar da awa biyu saboda azumin watan Ramadan da ake yi yanzu.

Kakakin ofishin shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Isma’il Ibrahim, ne ya sanar da hakan yau Talata a Dutse babban birnin jihar , kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ya sanar.

ADVERTISEMENT

Alhaji Isma’il, ya ce ma’aikatan za su fara aiki daga karfe 9 na safe su tashi zuwa 3 na rana a tsakanin Litinin zuwa Alhamis , ranar Juma’a ma’aikatan za su fara aiki daga karfe 9 na safe zuwa karfe 1 na rana.

Ba kamar yadda suke aiki daga karfe 8 na safe zuwa karfe 5 na yamma ba.

ADVERTISEMENT