✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramos ya yi murnar buga wa Real Madrid wasa sau 600

Dan wasan baya Sergio Ramos ya buga wa kungiyar Real Madrid wasa sau  600 a wasan da Madrid ta doke Ajad 2-1 a gasar Zakarun…

Dan wasan baya Sergio Ramos ya buga wa kungiyar Real Madrid wasa sau  600 a wasan da Madrid ta doke Ajad 2-1 a gasar Zakarun Turai a ranar Laraba.

Dan wasan, wanda kuma shi ne Kyaftin din Real zai zama saura wasa daya ya kamo yawan wasan da Fernando Hiero da Paco Gento suka yi wa Madrid kamar yadda BBC ya rawaito.

Ramos mai shekara 32 zai zama na hudu a jeren wadanda suka buga wa Real wasanni da dama, bayan Manolo Sanchis mai 710 da Iker Casillas mai wasa 725 da kuma Raul Gonzalez mai wasa 741.

Ramos ya koma Real Madrid da taka leda ne daga Sebilla a shekarar 2005.