Da Dumi Dumi

Rana daya za a yi zaben Gwamna da na Sanatan Kogi ta Yamma  – INEC

Daga Sanata Adeyemi da Sanata Melaye
Daga Sanata Adeyemi da Sanata Melaye

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ranar 16 ga Nuwamba mai zuwa za a gudanar da zaben Gwamnan Jihar Kogi da na Sanatan Kogi ta Yamma a tsakanin Sanata Dino Melaye na Jam’iyyar PDP da Sanata Smart Adeyemi na Jam’iyyar APC. A wani bayani da Hukumar INEC ta fitar dauke da sa hannu Mista Festus Okoye, ta ce za a hada zaben Sanatan da na Gwamna.

Ta ce gudanar da zaben ya biyo bayan soke zaben Sanatan Kogi ta Yamma da Kotun Sauraren Kararrakin Zabe da kuma Kotun Daukaka Kara suka yi ne, bayan karar da Sanata Smart Adeyemi na APC ya shigar.

Haka kuma za a gudanar da zaben cike-gurbi a mazabar Sabuwa a Jihar Katsina a ranar 30 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Share