Da Dumi Dumi

Ranar Ashura: An kashe mutum 8 a Kaduna da Bauchi

Kungiyar IMN ta ‘yan Shi’a mabiya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ta ce, jami’an ‘yan sandan Najeriya sun kashe mambobinta takwas a jihohin Kaduna da Bauchi yayin da suke tattakin ranar Ashura a yau Talata.

Kungiyar ta ce, an kashe mutum uku ne a jihar Kaduna a yankin Bakin Ruwa da ke hanyar Nnamdi Azikwe cikin birnin jihar.

Daya daga cikin shugaban Kungiyar IMN Aliyu Umar, ya shaidawa wakilin mu cewa, an kashe mambobin su ne a safiyar yau lokacin da suke suke tattakin ranar Ashura yayin da aka raunata wasu da dama.

Rahotanni daga jihar Bauchi, mabiya kungiyar IMN sun ce an kashe mambobin su biyar yayin da suke tattaki a birnin jihar da garin Azare da ke Karamar Hukumar Katagun.

Kakakin kungiyar IMN na jihar Bauchi Musa Boyi Mohammed, ya bayyanawa wakilin mu cewa, an harbe mambobin su hudu nan take sun mutu a garin Bauchi yayin da aka kashe daya a garin Azare tare da raunata wasu da dama.

ADVERTISEMENT
Share