✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar da na fara haduwa da Shata ya yi mini waka – dan Buram Tangale

“Sai’du dan Buram Tangale” Ambasada Alhaji Sa’idu Muhammad Fawu dan Buram din Tangale, tsohon Darakta ne a Babban Bankin Najeriya kuma Jakadan Najeriya a kasar…

“Sai’du dan Buram Tangale”

Ambasada Alhaji Sa’idu Muhammad Fawu dan Buram din Tangale, tsohon Darakta ne a Babban Bankin Najeriya kuma Jakadan Najeriya a kasar Indonesiya. Yana daga cikin mutanen da marigayi Alhaji Dokta Mamman Shata Kastina ya yi musu waka, sai dai ya ce a ranar da ya fara haduwa da Shata wajen bikin nadin kanensa a sarauta ya yi masa waka:

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?
Ambasada Sa’idu: Ni mutumin Jihar Gombe ne kuma an haife ni a garin billiri a ranar 1 ga Janairu 1944, na fara firamare a billiri a 1951 sannan na karasa a babbar firamare ta Gombe a 1956. Sai na babbar sakandaren Bauchi 1959 daga nan na tafi Yola na samu babbar takardar shaidar kammala sakandare (HSCE) a 1965, na samu yabo biyar na tafi Jami’a a Kano ni da Idris Bamai muka yi digiri daga 1967-1970. Da na gama sai aka dauke ni aiki a Jihar Arewa maso Gabas a bangaren sha’anin mulki a 1975, sai aka dawo Jihar Bauchi na zama Babban Sakatare a 1979 a shekarar 1988 aka mayar da ni Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da na shekara biyu sai na koma Babban Bankin Najeriya (CBN) har na zama Darakta, a shekara ta 2000 kuma na zama Ambasada a kasar Indonesiya a shekara ta 2003 zuwa 2005 na yi aiki a Hukumar Rabon Arzikin kasa (RMAFC), karo na biyu kuma zan yi ritaya a watan Nuwamban shekara ta 2015.
Aminiya: Kana daya daga cikn mutanen da marigayi Shata ya yi musu waka a ina ka hadu da shi ya yi maka waka?
Ambasada Sa’idu: Kafin Shata ya yi min waka ina jin sunansa ne kawai ban taba yin ido hudu da shi ba. Amma da yake komai kaddara ne, bayan na zama Dan Buram din Tangale da dadewa sai aka bai wa kanena Baraden Tangale, lokacin yana Darakta a Ma’aikatar Gona ta Tarayya, inda duk wani mai jigilar taki yana karkashinsa. Da aka zo bikin sarautar sai ya gayyaci abokansa cikinsu har da wani mai suna Hadi Sani wanda shi ya gayyato Shata zuwa bikin. Baya ga Shata, mawaka da dama sun hallara da yamma aka yi rawa a kofar gidan Galadiman Tangale, can misalin karfe 12:00 na dare sai Shata ya fara wake Hadi Sani. Can sai Hadi ya ce da Shata yaya zai zo garin mutane, amma bai yi wa wani waka ba shi ne a wannan ranar, watau 19 ga Disamban 1992, sai Shata ya dauko wakata ta:  “Sa’idu dan Buram Tangale.”  Yana wakar yana hadawa da rawar Tangale, bayan ya gama sai ya yi alkawarin cewa duk inda ya je sai ya yi wannan waka tawa, ka ji yadda aka yi Shata ya yi min waka.
Aminiya: An ce kudi ko mulki ba su sa Shata ya yi wa mutum waka, ko akwai kyautar da ka yi masa ne ya sa a wajen ya zabe ka ya yi maka wakar?
Ambasada Sa’idu: Watakila ya yi min ne saboda a gidana ake bikin ko kuma don saboda bikin kanena ya zo, amma dai akwai ’yan kyaututtuka da na yi masa da ya ji dadi, domin a lokacin ne aka fito da sabuwar takardar Naira 50, inda na ba shi bandir uku, wanda ya sa ya ji dadi. Amma wani lokaci ka san mawaki ko shiga zuciyarsa kawai ka yi ka burge shi, zai iya maka waka, ko ba ka ba shi komai ba, na san ba don wannan ’yan kudin ba ne ya yi wakar.
Aminiya: Me yake burge ka game da halayen Shata?
Ambasada Sa’idu: Shata ikon Allah ne, domin Allah Ya yi masa baiwa wacce ta zama masa sana’a, koda wane lokaci, ko da dare ko rana zai iya yi wa mutum waka ba tare da ya rubuta ko ya yi tunani a kai ba. Hatta wani abu daban wanda ba mutum ba Shata yana iya masa waka kuma ta tafi daidai, hakan yana matukar burge ni.
Aminiya: Ganin cewa ba kowa Shata ke yi wa waka ba yaya ka ji da ya yi maka waka?
Ambasada Sa’idu: Gaskiya wakar ta faranta mini rai, domin bayan ya yi mini wakar akwai lokacin da ya je Bauchi wasa, sai kawai aka ji ya dauko wakar da ya yi mini, sai wani abokina Alhaji Surajo Jibrin, ya bugo min waya yana tambayata a ina na san Shata har ya yi mini waka, alhali ko ka ba shi kudi in bai ga dama ba, ba zai maka waka ba? Shi ne na ce masa ya zo bikin kanena ne da aka nada shi Baraden Tangale, kuma hakan ya burge abokaina matuka.
Aminiya: Idan ka ji sunan Shata ko wakarsa da me kake tuna shi?
Ambasada Sa’idu: Ina tuna shi ne da mutumin da Allah Ya yi wa hikima Ya ba shi basira, domin mutum ne mai hikima kuma Allah Ya taimake shi duk wani abu na kuruciya ya daina su, domin wata rana ya fito daga Yola zai wuce sai ya tsaya a gidana a billiri muka ci abinci, yake ce mini yanzu kan tun da girma ta kama shi ya kamata ya daina duk wani shashanci ya koma ga Allah.