✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar dimokuradiyya

Yan Najeriya sun yi bikin 14 da dawowar mulkin dimokuradiyya, bayan da aka kawo karshen mulkin soja a ranar 29 ga Mayun shekarar 1999. Babu…

Yan Najeriya sun yi bikin 14 da dawowar mulkin dimokuradiyya, bayan da aka kawo karshen mulkin soja a ranar 29 ga Mayun shekarar 1999. Babu ko tantama, gwamnati da jami’an jam’iyya za fito da jerin nasarorin da suka samu tun daga kama ragamar mulki. ’Yan sun saba da bugun kirji wajen kanbama kawunansu; ko da kuwa abin da suka aikata bai taka kara ya karya ba. Yana da kyau a yi bukukuwa tunda har yanzu dimokuradiyyar ba ta wargaje ba.
Idan aka bibiyi wannan rana, ba ma tare da yin la’akari da al’amuran da suka wakna a shekara 14 tun daga shekarar 1999, za a fahimci yadda Najeriya ta kasance a ranar bikin dimokuradiyyar da aka gudanar a shekarar 2012. Za a fahimci matsayin da ’yan Najeriya suka kai wajen kiyaye ka’idojin dimokuradiyya a daukacin zabubbukan da aka gudanar a kasar tun daga shekarar 1999, inda daukacinsu suka karke da rikice-rikice. Masu rike da mukaman siyasa na cike da tsoro, don haka suka nuna gazawa wajen inganta al’amuran da za su inganta dimokurdiyya, ta yadda za ta samu gindin zama, ta ci gaba da bunkasa. ’Yan sanda ba su cika samun isassun kudin gudanar da ayyukansu, don haka sai abin da ’yan siyasa suka sanya su za su yi; hukumar shari’a an kassarata ta yadda manyan jami’anta suka samu kansu a cikin abubuwan kunya da suka saba wa doka.
Jam’iyyun siyasa, wadanda suka zama jigo wajen kyautata zamantakewar da za ta haifar da managarciyar dimokuradiyya, sun zama ja-gaba wajen kassara dimokuradiyya, musamman jam’iyyun da ke mulki.
Baya ga abin takaici, abin dariyar da aka yin a shirin shiga jerin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki nan da shekara ta 2020, babu wata manufa da aka tsara ta bunkasa tattalin arzikin kasa (wanda ke lakaki), an dakile shirye-shiryen bunkasa ilimi, babu dabarun bunkasa samar da abinci, ga karuwar rashin ayyukan yi, uwa uba tsaron rayukan al’umma ya zama babban kalubale.
Tattalin arziki a dabaibye yake da matsaloli, wadanda suka hada da wawushe asusun gwamnati da satar mai, al’amarin da gwamnati ta kasa shawo kansu, ga kuma nuna gazawa wajen aiwatar da tsare-tsaren kasafin kudi. A hakikanin gaskiya, hatta kasafin kudin shekarar 2013 da aka yi hanzari gabatar da shi a shekarar da ta wuce, wanda aka rika gani tamkar wadda azama ce da bude sabon babin dabarun sarrafa kudi, ya koma gaban Majalisar kasa, inda ake ta takaddama tsakanin fadar shugaban kasa da majlisa, kuma babu wata alama da ta nuna za a warware matsalar.
Nagartar shugabanci da ’yabn Najeriya suka yi has ashen samu a mulkin dimokuradiyya bai tabbata ba; al’amura sai kara tabarbarewa suke yi a irin wannan yanayin. Rashin kwarewa da gogewa a shugabanci ya bude kafar nuna bambancin kabilanci da rabuwar kawuana da rashin jituwar mabiya addinai, al’amarin da ya haifar da hadama da handamar tara abin duniya, ta yadda ake cutar da al’ummar kasa. ina dimokuradiyyar take, inda za a samu daidaito a tsakanin ’yan kasa da ’yancin yin walwala da hulda da juna da ’yancin shiga jam’iyyar siyasar da ta kwanta wa mutane a rai, tare da yin tasiri wajen sauya tsare-tsaren mulki, wadanda aka yi hangen nesa a a cikinsu, ba tare da kawo musu cikas ba?
Manufar raba mdafun iko a dimokuradiyya na fuskantar barazana . An yi rugu-rugu da mulkin kananan hukumomi. Gwamnatocin jihohi sun yi gaban kansu wajen kwace kason kudin kananan hukumomin, ko kuma su nada abokan huldarsu kan shugabancio. Mafi yawan kudurorin da aka gabatar a majalisa, ko a matakin jiha ko na kasa, sia kawia a yio watsi da su.
Aiwatar da dimokuradiyya ba ya nufin zabubbuka ba; yana nufin bayar da dama da daidaito, wajen raba lada da hukunci bisa la’akari da tanadin doka; babu dai wani abin farin ciki a cikin wannan al’amari. Daidaiton adalcin da masu rike da mukaman siyasa suka dauka shi ne, ’yan majalisa su yanke wa kansu albashi mai tsoka da alawus-alawus; su kuwa shugabanni su yi ta kashe kudi kan ayyukan da ba su da alfanu, alhali sun kasa biyan ma’aikatansu mafi karancin albashi na Naira dubu 18. Har yanzu akwai sauran aiki a gaban hukumar shari’a wajen tsame bara-gurbin da ke shafa mata kashin kaji, alhali ita ce mafita ta karshe ga talaka.
Idan har akwai wani darasi a cikin wadannan al’amura, to daya daga cikinsu, shi ne, dole ne gwamnati ta tsara al’amuran da suka dace ta fi bai wa fifiko, sannan ta yi kokarin warware matsalolin da suka addabi kasa.