✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar dimokuradiyya

Yan Najeriya sun yi bikin 14 da dawowar mulkin dimokuraxiyya, bayan da aka kawo qarshen mulkin soja a ranar 29 ga Mayun shekarar 1999. Babu…

Yan Najeriya sun yi bikin 14 da dawowar mulkin dimokuraxiyya, bayan da aka kawo qarshen mulkin soja a ranar 29 ga Mayun shekarar 1999. Babu ko tantama, gwamnati da jami’an jam’iyya za fito da jerin nasarorin da suka samu tun daga kama ragamar mulki. ’Yan sun saba da bugun qirji wajen kanbama kawunansu; ko da kuwa abin da suka aikata bai taka kara ya karya ba. Yana da kyau a yi bukukuwa tunda har yanzu dimokuraxiyyar ba ta wargaje ba.
Idan aka bibiyi wannan rana, ba ma tare da yin la’akari da al’amuran da suka wakna a shekara 14 tun daga shekarar 1999, za a fahimci yadda Najeriya ta kasance a ranar bikin dimokuraxiyyar da aka gudanar a shekarar 2012. Za a fahimci matsayin da ’yan Najeriya suka kai wajen kiyaye qa’idojin dimokuraxiyya a xaukacin zavuvvukan da aka gudanar a qasar tun daga shekarar 1999, inda xaukacinsu suka qarke da rikice-rikice. Masu riqe da muqaman siyasa na cike da tsoro, don haka suka nuna gazawa wajen inganta al’amuran da za su inganta dimokurxiyya, ta yadda za ta samu gindin zama, ta ci gaba da bunqasa. ’Yan sanda ba su cika samun isassun kuxin gudanar da ayyukansu, don haka sai abin da ’yan siyasa suka sanya su za su yi; hukumar shari’a an kassarata ta yadda manyan jami’anta suka samu kansu a cikin abubuwan kunya da suka sava wa doka.
Jam’iyyun siyasa, waxanda suka zama jigo wajen kyautata zamantakewar da za ta haifar da managarciyar dimokuraxiyya, sun zama ja-gaba wajen kassara dimokuraxiyya, musamman jam’iyyun da ke mulki.
Baya ga abin takaici, abin dariyar da aka yin a shirin shiga jerin qasashe 20 masu qarfin tattalin arziki nan da shekara ta 2020, babu wata manufa da aka tsara ta bunqasa tattalin arzikin qasa (wanda ke laqaqi), an daqile shirye-shiryen bunqasa ilimi, babu dabarun bunqasa samar da abinci, ga qaruwar rashin ayyukan yi, uwa uba tsaron rayukan al’umma ya zama babban qalubale.
Tattalin arziki a dabaibye yake da matsaloli, waxanda suka haxa da wawushe asusun gwamnati da satar mai, al’amarin da gwamnati ta kasa shawo kansu, ga kuma nuna gazawa wajen aiwatar da tsare-tsaren kasafin kuxi. A haqiqanin gaskiya, hatta kasafin kuxin shekarar 2013 da aka yi hanzari gabatar da shi a shekarar da ta wuce, wanda aka riqa gani tamkar wadda azama ce da buxe sabon babin dabarun sarrafa kuxi, ya koma gaban Majalisar qasa, inda ake ta taqaddama tsakanin fadar shugaban qasa da majlisa, kuma babu wata alama da ta nuna za a warware matsalar.
Nagartar shugabanci da ’yabn Najeriya suka yi has ashen samu a mulkin dimokuraxiyya bai tabbata ba; al’amura sai qara tavarvarewa suke yi a irin wannan yanayin. Rashin qwarewa da gogewa a shugabanci ya buxe kafar nuna bambancin qabilanci da rabuwar kawuana da rashin jituwar mabiya addinai, al’amarin da ya haifar da haxama da handamar tara abin duniya, ta yadda ake cutar da al’ummar qasa. ina dimokuraxiyyar take, inda za a samu daidaito a tsakanin ’yan qasa da ’yancin yin walwala da hulxa da juna da ’yancin shiga jam’iyyar siyasar da ta kwanta wa mutane a rai, tare da yin tasiri wajen sauya tsare-tsaren mulki, waxanda aka yi hangen nesa a a cikinsu, ba tare da kawo musu cikas ba?
Manufar raba mdafun iko a dimokuraxiyya na fuskantar barazana . An yi rugu-rugu da mulkin qananan hukumomi. Gwamnatocin jihohi sun yi gaban kansu wajen qwace kason kuxin qananan hukumomin, ko kuma su naxa abokan hulxarsu kan shugabancio. Mafi yawan qudurorin da aka gabatar a majalisa, ko a matakin jiha ko na qasa, sia kawia a yio watsi da su.
Aiwatar da dimokuraxiyya ba ya nufin zavuvvuka ba; yana nufin bayar da dama da daidaito, wajen raba lada da hukunci bisa la’akari da tanadin doka; babu dai wani abin farin ciki a cikin wannan al’amari. Daidaiton adalcin da masu riqe da muqaman siyasa suka xauka shi ne, ’yan majalisa su yanke wa kansu albashi mai tsoka da alawus-alawus; su kuwa shugabanni su yi ta kashe kuxi kan ayyukan da ba su da alfanu, alhali sun kasa biyan ma’aikatansu mafi qarancin albashi na Naira dubu 18. Har yanzu akwai sauran aiki a gaban hukumar shari’a wajen tsame bara-gurbin da ke shafa mata kashin kaji, alhali ita ce mafita ta qarshe ga talaka.
Idan har akwai wani darasi a cikin waxannan al’amura, to xaya daga cikinsu, shi ne, dole ne gwamnati ta tsara al’amuran da suka dace ta fi bai wa fifiko, sannan ta yi qoqarin warware matsalolin da suka addabi qasa.