✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Kiyaye Zaizayewar Kashi ta Duniya

Jibi Lahadi ne ake tunawa da zagayowar Ranar Ciwon Zaizayewar Kashi a duniya. A irin wannan rana a ko’ina a duniya ana fadakar da jama’a…

Jibi Lahadi ne ake tunawa da zagayowar Ranar Ciwon Zaizayewar Kashi a duniya. A irin wannan rana a ko’ina a duniya ana fadakar da jama’a musamman wadanda suka haura shekara 50 zuwa 60 kan wannan matsala ta zaizaiyewar kashi da yadda za su kiyaye aukuwarta ko rage mata kaifi. Maza da mata da suka haura wadancan shekaru suna cikin hadarin samun zaizaiyewar kashi, duk da cewa abin yakan fi kamari ga mata saboda karancin wasu sinadarai a jikinsu bayan an manyanta.

Me ake nufi da zaizayewar kashi? Mun riga mun san jikinmu na da kasusuwa da dama da suke rike da shi. Kuma tun a kuruciya wadannan kasusuwa suke haduwa su fara girma su kuma yi kwari sosai idan an fara tasawa. To bayan wannan kwari ne kuma kwatsam idan shekaru suka tunkaro maimakon kashi ya ci gaba da kara karfi sai ya tsaya cak, a wasu kuma daga nan sai ya fara zagwanyewa, kamar dai yadda gini ke rasa kwarinsa bayan wasu shekaru masu yawa.

To wannan zagwanyewa ta sinadaran da suka hadu suka gina kashin ita ake kira ciwon zaizayewar kashi. Kuma akalla a cikinmu mutane sama da kashi 70 cikin 100 ne ke samun matsalar in dai tsufa ya tunkaro, sai dai kawai na wani ya fi na wani, wato a wasu wadanda suka dau matakan kariya da wuri, wato a kuruciya da wuya ma a gane akwai matsalar.

Idan kaddara ta sa sai an samu matsalar, to alamomin da mutum wanda ya ba shekara 60 baya zai fara ji na cewa kasusuwa sun fara zagwanyewa sun hada da fara jin yawan ciwon jiki da alamu wadanda a gargajiyance akan dangantasu da tsufa kamar tashi daga zaune zuwa tsaye da kyar, zama da kyar, tafiya da kyar, daga nan kuma sai a fara rusunawa wajen tafiya, wato idan ana tafiyar ba za a iya tsayawa kyam ba.

A wadansu za a ga baya ya fara tankwarewa sun fara doro, wadansu kuma kafafuwansu su baude, ko su yi gwame, masu tsayi su ga tsayinsu na raguwa a sannu-a sannu. Daga nan sai a rika faduwa idan ana tafiya, wasu lokuta idan an fadi nan da nan za a samu karaya. Dama yawa-yawan abin da ke kawo karaya ga masu yawan shekaru zaizayewar kasusuwan wurin ne.

Yaya za a kiyaye ko kuma a rage kaifin ciwon? To tun a kuruciya dai ake fara gina kashi, wato tun daga yarinta. Yara da suka samu abinci mai gina jiki kuma masu gina kashi kamar madara da hanta da kifi masu dauke da sinadaran calcium da bitamin na rukunin D su suka fi kwarin kashi kuma su suke girma da kashi mai kwari wanda zai rage kaifin ciwon zaizayewar kashi. Sai yawan motsa jikin tun a kuruciyar shi ma yana taimaka wa lafiyar kashi.

To idan aka girma a haka ana samun wadannan abinci a kai-a kai kuma ana yawan motsa jiki, to kasusuwan na kara kwari sosai kamar yadda bulon da ya sha siminti da ruwa ke kara kwari.

Sauran abubuwan da za a yi la’akari da su idan ana so a kiyaye aukuwar matsalar su ne guje wa abubuwan da za su bata lafiyar kashi. Abubuwa masu bata lafiyar kashi kuwa sun hada da shan giya da busa taba sigari, sai kiba da shan kwayoyi masu sa kiba irinsu kwayoyin sha-ka-fashe na steroids. To idan aka guji wadannan, aka kuma bi waccan shawara ta samar wa kashin sinadaran gina shi, to ko matsalar ta zo, za ta zo da sauki.

 

Amsoshin tambayoyi

 

Ka amsa tambaya a kan abubuwan da ke sa warin baki. To ina za a je a magance shi idan mutum na da irin wannan matsala?

Daga M.B

Amsa: Idan mutum na fama da warin baki zai fara zuwa asibitin hakori ne ya ga likitan hakori, wanda shi ne likitan baki gaba daya. Daga nan idan ya ga wani abu sai ya yi maganinsa, idan ba zai iya ba zai tura mutum gaba

 

Shin yin amfani da kayan mai kyasbi zai iya sa mutum ya dauki kyasbi?

Daga Aminu Adamu Malam-Madori

Amsa: Eh, idan dai kyasbin kwayar cutar fungus ce ta kawo wa wancan mai ciwon za a iya daukar kwayar cutar. Tunda mun ce akwai nau’in ciwon kyasbi iri-iri, tun daga na kwayoyin cuta da na canjin yanayi da na borin jini da sauransu.

 

Mutum ne kasusuwa ke kara ya yi ta zufa da rama. Wane likita ya kamata a gani

Daga MGN, Katsina

Amsa: Mai samun wadannan alamu sai ya dangana da likitan sanyin kashi wato Rheumatologist a babban asibiti

Muna da ciwon basur tsawon shekaru. Wane irin likita za mu gani?

Daga Umar A. Kano da A. Sani da Abdulhamid Ahmed Bagiwa

Amsa: Likitan tiyata ya kamata ku gani

 

Shin taruwar miyau a bakin mutum lokacin barci matsala ce? Ko akwai abin da mutum zai sha ya rika samun raguwar haka?

Daga Hussain D. Katsina

Amsa: A’a ba matsala ba ce. Wadansu na iya samu a wasu lokuta a rayuwarsu kamar mata masu juna biyu, ko masu ciwon olsa. Amma wadannan ba da dare kadai yake taruwa ba, a koyaushe ne.

 

Da gaske ne amfani da kanwa a abinci yana iya kawo matsala ga lafiya?

Daga M. Darazo

Amsa: Eh, da yake gishiri ce haka ne yawan amfani da ita zai iya kara yawan gishiri a jiki. Ke nan sai dai a rika amfani da ita jefi-jefi

Idan aka yi mini allura sai in ji idanuna suna rufewa kamar ina jin barci amma ba barcin ba ne. Shin wannan matsala ce?

Daga Adamu Dankwambo, Abuja

Amsa: Eh, zai iya zama matsala saboda a da mun san akwai wata allura wai ita analgin da ake yi wa masu zazzabi mai sa irin wannan, amma a ’yan shekarun baya hukumomi sun haramta sayar da ita da amfani da ita saboda tana lalata idanu. Don haka duk asibiti ko kyamis da suke amfani da ita za ka iya kai korafi ofishin NAFDAC mafi kusa.