Search
Subscribe
Ranar Lahadi za a binne sirikin Ganduje

Ranar Lahadi za a binne sirikin Ganduje

A ranar Lahadi 28 ga watan Yunin da muke ciki za a binne tsohon Gwamnan jihar Oyo, sirikin Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, Marigayi Sanata Abiola Ajimobi.

Za a yi wa Marigayin sallar jana’iza ne a babban masallacinsa na  Oke-Ado da ke garin Ibadan a Jihar Oyo ranar Lahadi da misalin 12.00 na rana.

Mai magana da yawun tsohon gwamnan, Bolaji Tunji ne ya sanar da haka, yace matakin ya zo ne bayan wata ganawa da iyalan mamacin suka yi domin fitar da matsaya a ranar Juma’a bayan sun shawarci gwamnatin jihohin Legas da Oyo.

Sanarwar ta ce za a yi jana’izar ne cikin bin ka’idojin kare yaduwar COVID-19, za kuma a nuna jana’izar tashi kai tsaye ta kafar talabijin.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin