✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Sallah: Babu wanda zai shiga Kaduna daga Kano

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya shaida cewa babu wanda zai shiga jihar daga Kano a ranar sallar Idi karama. An ga gwamnan a…

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya shaida cewa babu wanda zai shiga jihar daga Kano a ranar sallar Idi karama.

An ga gwamnan a wani fefen bidiyo  yana shan alwashin cewa zai fita ranar salla ya datse hanyar da ta hade jihar Kano da Kaduna domin ya tabbatar babu wanda ya shigo saboda gudun kada a yada cutar annobar COVID-19 a Kaduna.

“Kuma ni ran salla zanje hanyar Kano inga wanda zai shigo Kaduna ranar, ni da kai na zanje.

“Duk ma mai wani shirin zuwa daga Kano ya sani ina nan ina jiran shi, kuma ba zan bar wurin ba sai dare yayi.

“Domin dole ne mu hana mutane wadanda su sun yi wasa da wannan ciwo, yabi gari yayi kanta kuma su kawo mana shi.

“Dole ne mu kare al’umar mu, abin da muke yi ke nan, mutane da yawa ba zasu ji dadi ba” in ji gwamnana El-Rufa’i.

Gwamna Nasiru El-Rufa’i na daukar wannan mataki ne bayan da takwaransa na Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bada sanarwar sassautawa al’umar jihar Kano dokar kulle a ranar sallah, tare da basu damar yin sallar Idi da ta Juma’a