A ranar Talata mai zuwa ce za a dawo Gasar Zakaun Turai da aka kwana biyu ana hutu tun kammala zagayen farko na gasar.
A ranar Talata 18 da watan Fabrairu za a fara fafata wasannin farko na zagaye na biyu na gasar.
Kungiyar da ke rike da kambin, Liberpool za ta bakunci kungiyar Atletico Madrid a birnin Madrid, don fafatawa.
Liberpool tana tashe a yanzu haka, ita kuma Atletico Madrid tana fama da kwan-gaba-kwan baya a wasa a bana.
Ana sanya Liberpoop a cikin kungiyoyin da za su iya lashe gasar, duk da cewa ita ce ta lashe gasar a bara.
Masu sharhi kan wasan kwallon kafa suna ganin tun lokacin da Liberpool ta lashe Gasar Zakarun Turai a bara, likafar kungiyar yake ta kara gaba.
A daya wasan kuma a ranar Talata, PSG ce za ta goge-raini da kungiyar Dortmund a Jamus.
Dukkan kungiyoyin akwai alamar a shirye suke, lura da yadda suke kokari a gasar gida da suke bugawa.
Sai kuma ranar Laraba, inda za a fafata atsakanin Atalanta da Balencia, sai kuma Tottenham ta fafata da kungiyar Leipzig a gidan Tottenham din.
Kasancewar Jose Mourinho ya karbi ragamar horar da Tottenham, wadansu na ganin kungiyar za ta iya bada mamaki a Gasar Zakarun Turai duk da cewa kungiyar na kwan-gaba-kwan-baya tun bayan da ya karbi ragamar daga tsohon kocin kulob din.