Da Dumi Dumi

Ranar ‘yanci ko ta ‘yan ci-rani?

 Wainar ‘yanci ko ta ‘yan ci-raniA shekaru babban lauje da kofar hanci da samun ’yancin kan Haurobiya, za a iya jero mata gurgun ci gaban da ta samu, wadanda suka hada da kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma, al’amari da kamarin ya kai ga ana ganin tana cikin sahun farko, a jerin kasashen da jaba da gafiya da kusu ke wadaka. Ta zama kasar da aka yi kiki-kaka, domin jami’an Asusun ilimi sun yi yaji an gaza bikonsu; manyan masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai sun yi zaman dirshan a gida.
A kasar Haurobiya da wuya safiya ta yi zuwa almuru ba a samu labarin wasu almurawa sun salwantar da rayuka da dukiyoyi ba, musamman a Jihar su Alan-guburo da ta Yawon-Bebe.
A wajen raba romon dama-dama da kurda-kurdar wasoson Samson-siya-siya kuwa, an yi rugu-rugu da masakun tufafi, tare da durkusar da manya da kananan masana’antu, al’amarin da ya haifar wa matasa masu jini a jika gadin layi, suna ta gararamba a gari, wanda duk ya samu aiki ko na tada kan adda ne, sai kawai ya tsunduma ciki, ba tare da la’akari da abin da zai je ya komo ba.
Wata gwaggwabar nasarar da aka samu, ita ce ta wargaaza hadin kan talakawa, aka jefa su cikin sasarin talalar talauci. A halin yanzu dai kasa ta zama jamhuriyar ja-ni-ina reto, ko ma a ce jamhuriyar dundumdurundum, tunda an cefanar da kamfanin dundumdurundum, bayan an salawantar da Hauro tiren taliya kofar hanci wajen kara jagwalgwala shi.
Duk wanda zai yi batu na-ingarman karfe, dole ne ya ce, ‘Haurobiya ta cirri tuta wajen aiwatar da ayyuikan batan-baka-tantan.’
Ranar ’yancinmu dai ta zama ranar ’yan ci-rani. Baba-ojo ya yi ci-rani a gadon mulkin Haurobiya, sai marigayi Shugaba ’Yar’bishiya, wanda bai dade yana cin-rani ba, ya yi kaura daga wannan duniyar. Sai kuma yau ga Shugaba Jatau Mai-sa-in-sa ya ci-ranin, maimakon ya kauce wani ya zo, ya yi nasa, ya doge kan lallai babu wanda zai hana shi ci gaba da rani. To ni dai na san damina ta fadi, kuma a labaran Amintattar jaridar kasar Haurobiya, an taba bayyana yadda ‘Damina ta jawo damuwa; haka ma rani zai iya zama rauni; kaka za ta iya zama kiki-kaka.
Ni dai na san Mamman sarkin tausasa kidi a birnin Dikko, ya taba furta cewa: “Nufinsu mu yi wasan gargajiya ya sa mu kara fahimtar juna, amma wasu sun bar al’adun na iyayensu sun bi na ’yan ci-rani.” Duk da cewa ni Direban alli ne, bai kamata in tsaya faskaren ma’anoni ba. Da fatan kow aya je Gano a wannan gabar. Kai ina sa ran ma wasu za su yanki tikitin tsuntsun sama zuwa kasar Ghana.
Idan har ’yan makaranta ba su ari faden Malam Mantau ba, to za su fasko yadda muka zayyana batutuwa kan dabarun Damo-da-kura-da-diyya, wanda jam’iyya mai dan boto da sand ajirge ta kware a kai. A daidai lokacin da ake murnar zagayowar ’yancin Haurobiya na shekara ta babban lauje da kofar hanci, ’ya’yan mai dan boto da sanda jirge suka raba rana, inda bangaren Banga-Banga Tukururu ke artabu da Kawun Bararrejewa.
Idan har Haurobiyawa za su bibiyi kundin labarin da, da na yanzu, watakila za su fara karatu daga shekara ta alif sili da manuniyar kasa da ta sama da zagaye, wato zamanin da Sarauniyar Birtaniya ta sarayar ikont ana mulkin mulaka’u a kan Haurobiya, ta mika wa Malam Na-Tafawa abin faharin Haurobiyawa, inda ya Hadu da Zakin fama da gungun masu kishin al’umma da kasa wadanda suka hada da Aminin siyasar Kanawa da Sarkin-daukar-dawainiya, Gamji giji-giji, uban masu bobo da kwambon bokoko.
Kundin labaran da ya zayyana mana yadda son rai da zalamar tara abin duniya suka sanya Haurobiyawa suka yi rugu-rugu da kasarsu, bayan da iyayen al’umma suka yi kaura da wannan duniyar. kasar nan ta hau turbar batan-baka-tantan ne a daidai lokacin da gama-garin al’umma suka saki layi. Zabi dai ya rage ga mai shiga kwakware, ko dao mu koma da baya, mu hau kan turba, ko kuma mu ci gaba da tabarbarewa.
Wanda duk ba ya son tabarbarewa da tabewa, to ya himmatu wajen tarairayar rayuyka da dukiyoyin al’umma, ta yadda za a tabbatar da adala a kan kasa. Masu fuskantar alkibla, ku fuskanci batu na-ingarman karfe, a yi komai keke da keke. Ku kuwa masu addu’a da gicciye, ku yi kokarin gicciye zalunci da son rai, ta yadda za a tabbatar da kaunar juna a tsakanin al’ummar Haurobiya.
kiri da muzu taro da far-far-a-titi ya gagara gudanarwa a dandalin mikiya, inda Shugaban kasar Haurobiya ya yi bikinsa shi da mukarrabansa a cikinfadar tsaunin bila. Shugabanni sun nuna gazawa wajen aiwatar da tsare-tsaren tsimi da tanadi; da kyautata zamantakewa, sabanin haka sai zaman takewa ake ta yi.
Arewatawa tunda ku kuka fi kowace al’umma a Haurobiya fadawa cikin balbalin bala’i, ina ganin mfitarku ita ce baitukan wani mawaki, wato:
Lallai, lallai akwai gyara
Yau ga malamin gona
Iri mai kyau, ya zan abin shuka…
Wadanda suka iya faskaren wannan waka, sais u fara fafutikar ganin an rage laluben lagwadar man tunkuza, a himmatu wajen kafa Jamhuriyar Hauren-Hatsi, musamman ma jin cewa “hantsi in ba hatsi hadari ne.” Mu roki Mai-duka ya yi mana maganin hautsinewa.
Mu daina jefa azargagiyar zargi a kan mai danboto da sanda jirge, domin yau an gansu a rana. Mu kyale Shugaba Jatau Mai-sa-in-sa, ya je ya ci gaba da sa-in-sa da Haurobiyawa da su In-gwan-gwaje-in wala, ta yadda zai ci gaba da yi mana wala-wala; ga mace zane; ga Masanin sisi-da-sisi, wadanda ke tsara wa gwamantin Haurobiya yadda za ta ci gaba da jikkata talakawanta. daukacin wadannan mutanen da aka zayyano, ya kamata a basu lambar yabo da kwarewa wajen kassara al’umma da kasar Haurobiya, musamman a daidai irin wannan lokaci da muke bikin rashin ’yanci, don mun zama ’yan ci-rani.’

Share