✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar ’Yancin Kai: Ba Biritaniya ce ta jawo koma-bayan Najeriya ba –Farfesa Ayagi

Farfesa Ibrahim Ayagi tsohon ma’aikacin banki ne kuma Shugaban Kwamitin Tattalin Arziki (NIEC) a zamanin mulkin Cif Obasanjo. A wannan tattaunawa ya yi magana kan…

Farfesa Ibrahim AyagiFarfesa Ibrahim Ayagi tsohon ma’aikacin banki ne kuma Shugaban Kwamitin Tattalin Arziki (NIEC) a zamanin mulkin Cif Obasanjo. A wannan tattaunawa ya yi magana kan abin da ya sa Najeriya ba ta ci gaba a matsayin kasa da bukatar da ke akwai na dorewar tsare-tsare da sauran batutuwan da suka shafi kasa:

Daga Lawan danjuma Adamu da Salihu Makera

Najeriya tana bikin cika shekara 53 da samun ’yanci a wannan mako. Akwai wani abin doki ga’yan Najeriya don murnar 1 ga Oktoba?
Ka san kowa da irin fahimtarsa kan ’yancin kai. Ina tunawa lokacin da muka samu ’yanci a ranar 1 ga Oktoban 1960 na yi farin ciki sosai a bikin farko. Ya sanya abubuwa da dama a zuciyata da ya kamata mu cimma. Birtaniya ke mulkarmu sai ga shi lokaci ya zo muna karbar mulkinmu. A wancan lokaci ba mu san abubuwan da muka sani a yanzu ba, amma muna tunanin abin da zai kasance namu da abin da za mu cimmawa.
Da wannan, abubuwa suka rika zuwa suna wucewa, kowannemu yana kokarin cimma abin da ya sa a gaba. Sai sojoji suka yi katsalanda ga dimokuradiyyya. Gwamnatin farar hula da ta karbo ’yancin aka kawar da ita, sojojin da suka zo suka ce za su yi abin da ya fi na farar hula da ’yan siyasa kyau. Kuma mun ga abin da suka yi, sun ba da kunya ga da dama daga cikinmu.
A duk lokacin da bikin ’yancin kai ya kewayo mukan yi murna. Mutane irinmu da muka yi ta murna daga farko yanzu muna gani al’amura sun tabarbare. Abubuwa sun fara canjawa da su sojojin da sauransu. Mun fahimci ba mu cimma fatarmu ba, saboda ba mu samun nasarar da ta kamata. Sai tunani game da ’yancin kai ya fara canjawa. Akalla tunanina game da ’yancin kan ya fara canjawa, na fara nuna rashin farin ciki kan samun ’yancin. Haka ya ci gaba har aka kai wannan lokaci da mutum bai nuna damuwa da bikin samun ’yanci. Wannan saboda fatar da muke da ita ta rushe, mun samu kanmu a yanayin da ba mu tsammani, don haka babu wani doki ko farin ciki kan samun ’yancin kai.
Yanzu ranar samun ’yancin kai, kan zo ba wanda zai tuna ya aika maka katin taya murna, kai ma ba za ka taya wani murna ba. Sai dai duk da cewa mutane da dama ba su dokin bikin samun ’yancin kai, ba za mu so mu koma baya kamar 1960 ba. Gaskiya ’yanci yana da muhimmanci, saboda akalla muna mulkin kanmu, duk da cewa mu gaza cimma manufofinmu.
Wasu alamu ake da su a wancan lokaci da suka sa jama’a ke ganin akwai alfanu ga samun ’yancin kan Najeriya?
A wancan lokaci na samun ’yancin kai muna jin Birtaniya ke mulkarmu, kuma sun takaita mana wasu abubuwa kan abin da za mu yi da mutanen da za mu hulda da su. Misali, za mu yi kasuwanci ne kawai galibi da Birtaniya. Duk kayayyakinmu da wadanda za mu shigo da su duk sun shafi Birtaniya ne kafin samun ’yancin kai. Muna tunani idan muka samu ’yanci, kasuwarmu za ta bude a duniya; za mu iya kai kayayyakin da muka sana’anta ga kowa, ta yin haka kasuwarmu za ta rika haifar da riba tana bunkasa. Wannan abin alheri ne. Kuma za mu iya zuwa kasuwar duniya mu yi ciniki da mutanen da muka so wadanda suke sha’awar kayayyakinmu. Wannan shi ne tunaninmu; duk da cewa mun san Birtaniya tana da son zuciya. Muna jin kasancewar akwai mutanenmu a gwamnati, za su yi duk abin da ya kamata domin amfanin Najeriya da ’yan Najeriya. Mun dauka za mu fito a duniya, mutane su rika zuwa nan. Kasan burin ’yan mulkin mallaka na farko shi ne, su ilimantar da mu ta yadda za mu taimaka musu su mulki Najeriya. Wannan shi ne kawai abin da suke so da ilimantar da mu. Alhali kuma ilimi ya wuce haka; mu a kanmu muna son ilimantar da kanmu domin bunkasa kasarmu. Mun dauka za mu bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta yadda zai iya goga kafada da na Birtaniya da sauran kasashe. Mun so mu gina kakkarfan tattalin arziki, wannan shi ne abin da muke da sha’awa a kai.
Laifin rashin ci gabanmu na mutanen Birtaniya ne ko na shugabanninmu ’yan kasa?
Ban taba dora laifin koma bayanmu kan mutanen Birtaniya ba. Ba na ganin haka a matsayin laifinsu. Lokacin da muka samu ’yancin kanmu, mun san burinmu da abin da muke so. Shugabanninmu ma sun san abin da muke so, duk da cewa mun hadu da masu mulki iri daban-daban a shekara 53.
Kamar yadda na fadi, shugabannin – sojoji da farar hula – sun zo da dabaru daban-daban da mahanga daban-daban kan abin da za su yi. Don haka ban taba sukar wani daga wajen Najeriya ba. Mun gaza cimma abin da ya kamata mu cimmawa ne saboda ’yan Najeriya. Ba zan ce saboda shugabanni kadai ne muka kasa ci gaba ba, akwai dalilai da dama kan abin da ya hana mu ci gaba. A Najeriya muna da matsalar shugabanni da na mabiya. daya daga cikin manyan matsalolin, wanda abin takaici ke tare da mu na tsawon lokaci shi ne almundahana. Almundahana ita ce matsalar Najeriya. Tambayar ita ce: “Wane ne bai yin almundahana a Najeriya? Amsar tana iya zama mai almundahana shi ne wanda aka kama. Amma akwai ’yan almundahana da dama da ba a kama ba.
Ba wai ina cewa kowa a Najeriya ya lalace ba ne, misali ni ba na almundahana kuma na san akwai mutane da dama da ba su yin almundahana. Almundahana ke dakile mu daga ci gaba. Man fetur dinmu ana ta sace shi a sayar a kasuwar duniya. kasashe kalilan ne irin haka ke faruwa. To da irin wannan matsala zai yi wahala a ci gaba.
To, matsalar ba ta shugabannin ne ko mabiya ba kawai, tasu ce su biyun. Ana iya cewa babban aikin gwamnati shi ne ta samar da shugabanci nagari; don haka mutanen da suke cikin gwamnatin ne galibi ake dora wa laifi idan kasa ba ta ci gaba. Kuma ba mu ci gaban ba.
Idan ka dauki misalin kasashen da ke Asiya kamar Singapore da Indonesiya da China da Indiya, duk sun ci gaba sosai, kuma suna tsere da kasashen da suka ci gaba. Ko Indiya tana tsere da kasashen da suka ci gaba duk da cewa tattalin arzikinsu yana da matsaloli. Suna fama da talauci, a kwanakin baya sun bullo da wani shirin abinci inda ake ba mutane da dama abinci duk wata. Suna kashe tiriliyoyin rupee din kasar don ciyar da jama’a, ba su shigo da abinci, suna noma abincin ne. A Najeriya mun gaza ciyar da kanmu, da yawa abin da muke ci ana shigo da shi ne. Ka ga ba mu iya noma isasshen abinci don ciyar da kanmu, wanda hakan matsala ce.
Mu tuna Indiya tana da kusan mutum biliyan biyu, nakan yi tunani cewa matsalar Najeriya yawan jama’a ce; to amma sai na ga Indiya da China suna ci gaba. Tattalin arzikin China yana daya daga cikin wadanda suka fi karfi a duniya, Indiya ma tana ci gaba. Hatta kasashe kamar Malesiya da ta zo nan kasar a wajejen 1960 ta dauki irin kwarar manja, yanzu tana samun kudi da shi tana ci gaba.  Su ba kamar Najeriya ba ne, a Najeriya ba za ka iya daukar abu daya ka ce muna ci gaba a wannan ba. Babu, ba za ka samu wannan ba. Muna surutu da yawa kan abin da muke so da abin da muke yi, amma a zahirin abubuwa za ka ga muna komawa baya ne. Mukan bullo da shiri amma ba mu iya dorewa da shi. Ba mu dorewa a abu kowa ya zo sai ya bullo da nasa daban. Muna da shirye-shirye barkatai kamar yadda muke da shugabannin. Alhali abin da muke bukata shi ne dorewar ci gaba tattalin arziki. Wannan dorewar ci gaban tattalin arziki ya zame mana matsala. Yanzu ga shi muna fama da talauci, matsalar rashin aikin yi da sauran matsaloli. To yaya za a yi da matsalolin?A yi irin yadda “Damisoshin Asiya” suka yi.
A Najeriya ana kashe kashi 70 cikin 100 na kasafin kudin shekara kan ayyukan yau da kullum, babu isassun kudin yin muhimman abubuwa. Alhali nan ne inda ya kamata kudi ya rika zuwa – manyan ayyuka. Idan ba a yin manyan ayyuka ba za a ci gaba ba. Yanzu muna da gwamnatoci da dama – na tarayya da jihohi da kananan hukumomi – dukkansu suna kashe kashi 70 na kasafinsu na shekara kan ayyukan yau da kullum. Ayyukan yau da kullum manufarsu bai wuce abin da ake kashewa marar kawo riba ba, kamar biyan albashi da kudin da ake kashewa yau da gobe. Kana kara samunsu kana kara kashe su, ba su kawo wani ci gaba. Wadannan abubuwa ana ci gaba da yin su, saboda sun shafi batarwa ne. Misali idan ka gina hanya dole ka kula da ita, tana cin kudi ne kawai, ka gina makarantu; duk da cewa tana ba da ilimi, kana bukatar kudin kula da ita. To kana kara kashe kudi ne kan ayyukan yau da kullum kana rasa na gudanar da manyan ayyuka masu kawo kudi. Alhali abin da ake bukata shi ne ka samu kudin da za ka kashe kan manyan ayyuka, ka yi manyan ayyukan da za su yi abubuwan da mutane ke bukata. A yanzu ina jin Najeriya kasa ce da ta fi batar da kudi don ci, shi ya sa mafi yawan kudin ke tafiya kan ayyukan yau da kullum ana batarwa, wannan ba zai kai mu ko’ina ba.Maciya kawai muke da su da ba su barinmu da ragowa don zubawa a manyan ayyuka. Wannan ya sa ba mu ci gaban da ya kamata. Ba wai muna sukar gwamnati ne ba, mutane suna cewa wannan shi ne dimokuradiyya kuma wajibi ne gwamnati ta samar musu da abin da suke kira romon dimokuradiyya.  Romon dimokuradiyyar ne, ni da kai muke cinyewa. Alhali bai kamata a takaita shi a haka ba. Kamata ya yi wannan romo ya hada da samar da manyan abubuwa da za su iya samar da kayayyakin da za a yi amfani da su domin sarrafa wasu abubuwa. Mafi yawan kayan da muke bukata a kasar nan shigo da su ake yi daga waje; alhali za mu iya yin su a nan. Wannan ne ya sa muke komawa baya. Domin zama kamar kasashen Asiya na bukatar mu tambayi kanmu: “Me muke yi? Shin muna kan tafarki a yanzu? Za mu kai gaci kuwa ta bin wannan hanya?”
Eh, daya daga cikin manyan matsalolin da muke da su shi ne karuwar jama’a. Najeriya tana karuwa da sama da kashi uku cikin 100 kowace shekara. Yanzu mun kai mutum miliyan 150 nan da shekara 25 za mu iya kaiwa miliyan 300. Kuma albarkatun da ake da su ba su wadatar mutane. Don haka wajibi ne mu bunkasa wasu fannonin da za su rika samar da abubuwan da jama’a ke bukata. Idan ka samar da mutane, dole ka samar da aikin yi. Amma yanzu ga mutane nan suna yawo babu abin yi. Mutane na karuwa aikin yi na raguwa dole mutane su kara talaucewa. Kuma in aka bar lamarin haka talauci da rashin aikin yi ne za su ci gaba da karuwa. Wannan kuma bai dace ba.