Fitaccen mawakin Jam’iyyar APC da Shugaba Buhari Dauda Kahutu Rarara ya gwangwanje dan wasan barkwanci Shagiri Girbau na Kano da sabuwar babur.
A wani faifan bidiyo da hutuna da Aminiya ta gani, an nuna lokacin da Rarara yake mikawa Shagiri Girbau mabudin babur din, sanna shi kuma yake masa godiya.