Da Dumi Dumi

Rashford ya yanke shawarar ci gaba da zama a Man United

A ranar Talatar da ta wuce ne dan kwallon gaba a kulob din Manchester United na Ingila Marcus Rashford ya bayyana cewa ya gwammace ya ci gaba da zama a kulob din Man United maimakon ya koma kulob din Real Madrid da ke Sifen.

Dan kwallon wanda ya so komawa Madrid a lokacin tsohon kocin United, Jose Mourinho, ya ce a yanzu ya canja shawara ganin yadda tauraruwarsa ke haskakawa.

Jaridar UK Sun da ake bugawa a Ingila ta kalato cewa Rashford yana jin dadin buga wasa a karkashin sabon koci Ole Gunnar Soljskaer inda a wasa uku ya samu nasarar zura kwallaye biyu.

Rahotanni sun ce tun a watan Nuwamban bara  mahukunta kulob din Madrid suke yunkurin saye dan kwallon daga Man United saboda rashin buga wasa a kan kari a karkashin Jose Mourinho. An ce Madrid ta nemi sayen dan kwallon ne a wannan wata bayan an bude kasuwar cinikin ’yan kwallo.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya